Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi dake ziyara a Amurka, ya gana jiya da takwaransa na kasar Antony Blinken, inda ya ce akwai bukatar kasashen biyu su daidaita dangantakarsu tare da komawa bisa tafarki mai aminci da karko da dorewa, nan ba da jimawa ba.
Wang Yi ya bayyana haka ne yayin da shi da Anthony Blinken ke tattaunawa da manema labarai kafin ganawarsu su biyu.
- Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Kama Hanyar Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba A Yankin Tsaunin Himalaya
- Kamata Ya Yi Gwamnatin Amurka Ta Yi La’Akari Da Dalilan Karbuwar Gwamnan Jihar California A Kasar Sin
A cewarsa, bisa gayyatar da bangaren Amurka ya yi masa, ramako ne ga ziyarar Anthony Blinken a kasar Sin a watan Yunin da ya gabata. Ya ce manyan kasashen biyu na da bambamce-bambance, haka kuma suna da muhimman muradu da kalubale iri guda dake bukatar a shawo kansu. A don haka, Sin da Amurka na bukatar tattaunawa. Yana mai cewa ba sake fara tattaunawa kadai ba, akwai bukatar zurfafa tattaunawar da inganta fahimtar juna da rage sabani da mummunar fahimta.
Wang Yi ya kara da cewa, tabbas za a ci gaba da samun surutai game da huldar Sin da Amurka, kuma kasar Sin za ta tunkari batun cikin lumana, saboda ta yi imanin cewa, bambance gaskiya da akasinsa, bai dogara da karfin kwaji ko na murya ba, sai dai ko an kiyaye tanade-tanaden yarjejeniyoyin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu da dokokin kasa da kasa da yanayi na ci gaba da ake ciki. Bugu da kari, ya ce sun yi ammana cewa, gaskiya da tarihi, za su ta tabbatar da komai.
A lokacin da Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaransa na Amurka Antony Blinken, suka yi musanyar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da wasu abubuwan dake jawo hankalinsu tare. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha, Amina Xu)