Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yiwa manema labarai karin haske, game da halartar babban taron kungiyar BRICS karo 16 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, a birnin Kazan na kasar Rasha, tsakanin ranakun Talata da Alhamis.
Bayan dawowa gida, Wang Yi ya ce an cimma cikakkiyar nasara, yayin da shugaban kasar Sin ya halarci wannan muhimmin taro na BRICS, wanda hakan ya nuna yadda Sin ta sake taka muhimmancin rawa, a matsayin kashin bayan hadin gwiwar BRICS, kuma muhimmiyar mamba cikin gamayyar kasashe masu saurin samun ci gaba da masu tasowa.
- Musabbabin Lalacewar Lantarki A Jihohin Arewa -TCN
- Hatsarin Jirgi Ya Sa Mataimakin Shugaban Kasa Ya Soke Ziyarar Amurka
Wang Yi ya kara da cewa, a wannan karo, shugabannin kasashe sama da 30, sun hallara a birnin Kazan, don halartar taron tattaunawa na “BRICS+”, sun kuma gudanar da tattaunawa mai zurfi, game da zurfafa tasirin mabanbantan sassan duniya, da ingiza adalci a fannin ci gaba, da samar da tsaro tsakanin kasa da kasa, da kara fayyace burin wannan rukuni na kasashe, na wanzar da zaman lafiya da tsaro, da neman tafarkin ci gaba da wadata, da fatan samar da daidaito da adalci.
Daga nan sai Wang Yi ya jaddada aniyar kasar Sin, ta kara dinke kungiyar BRICS da sauran sassa abokan huldar kasashe masu tasowa, da hada karfi da karfe da sassan kasa da kasa, wajen ci gaba da cimma burikan da aka sanya gaba, a sabon tafarkin bunkasuwa da sake farfadowa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)