An kama wani mutum a Pakistan bisa zargin kashe ‘yarsa budurwa bayan ta ki daina dora bidiyonta a TikTok, kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Alhamis.
A cewar shugaban ‘yansandan yankin, Babar Baloch, wanda ake zargin, wanda shekarunsa sun kusa kai 50, ya kwaso iyalansa ne daga Amurka kwanan nan zuwa Quetta, wani birni a kudu maso yammacin Pakistan.
- TikTok Ya Dawo Aiki A Amurka Bayan Matakin Da Trump Ya Ɗauka
- Rundunar Ƴansandan Kano Ta Kori Wani Jami’i Saboda Karɓar Na Goro
Baloch ya bayyana cewa, mahaifin ya amsa laifin harbe diyarsa a farkon makon nan bayan ta ki sanya tufafi da suka dace da addini da al’ada da kuma daina yada bidiyo a dandalin sada zumunta.
Baloch ya ce “Na amince da laifin kashe ‘yata, saboda abinda take yi, zubar da mutuncin dangina ne.”
‘Yansandan dai tuni suka sanya shari’ar cikin wani lamari na ‘kisan mutuntaka’, wacce al’ada ce ga ‘yan uwa, musamman maza, ke kashe mata, wanda suke imanin cewa, sun kawo “abin kunya” ga danginsu.