Isah Barde, matashi dan shekara 17 da ya kammala makarantar sakandire a jihar Kano, ya kera Mutum-mutumi mai motsi (Robot) ta hanyar amfani da kwali da bututu da ledodi da alminiyom da injinan wutar lantarki dai sauransu don taimaka wa robot din bin umurnin gudanarwa.
Isah ya kasance yaro mai sha’awar shiga fannin nazarin fasahar kere-kere sai dai ya bayyana cewa yana da matsalar kudade wajen cigaba da samun horo a fannin.
Shekaru uku kenan da matashin ya fara kera na’urar mutum-mutumi, wanda ya bayyana a matsayin wani bangare na burin rayuwarsa, duk da karancin tallafi.
Barde ya shaida wa Trust TV cewa, Yana sarrafa robot din ne ta hanyar motsa hannayensa