Daga A.A.Masagala,Benin
Wani saurayi mai suna Ali ya sarewa abokinsa mai suna Muhammed Abdullahi kai da adda a yayin da ya kai masa ziyara awurin aikinsa na gadi daura da babban titi daga Benin zuwa Auchi ta jihar Edo.
A yadda wan nan lamarin ya faru kamar yadda shi Muhammed Abdullahi din ya shaidawa Leadership A Yau bayan faruwar lamarin cewa, da misalin karfe 7:45 na dare “na je wurin wannan abokin nawa Ali muna zaune inda lebirori suke haduwa da dare suna tayashi hira kamar yadda suka saba nima na saba ina zuwa wurinsa saboda haka shine dalilin da ya janyo man wannan wahala” sai kuma kara cewa ‘’Da yake wajen da abin ya faru ba shi da nisa da Ofishin ‘yan sanda sai na je na shaida musu”
Duk irin kokarinda Leadership A Yau ta yi domin samun karin bayani daga bangaren hukumar ‘yan sandan ta jihar bai samu nasara ba.