A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi a gaban kusan daukacin shugabannin kasashen Afirka, inda ya yi amfani da wani karin magana na Afirka wajen siffanta huldar dake tsakanin Sin da Afirka, wato “Mai buri daya shi ne aboki na gaske.”
A jawabin nan da shugaba Xi ya gabatar a bikin kaddamar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2024 da ke gudana a birnin Beijing na kasar Sin, shugaban ya ambaci buri daya da Sin da kasashen Afirka suke da shi, wato zamanantar da kansu.
- An Zartas Da Sanarwar Beijing Da Tsarin Aiki A Taron FOCAC
- Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude Taron Kolin FOCAC
Sai dai wane irin zamanantarwa ake bukata? A cewar shugaba Xi, ya kamata a yi kokarin samun zamanantarwa cikin adalci, da bude wa juna kofa da cin moriyar juna, da mai da jama’a a gaban kome, da kare muhallin halittu, da zaman lafiya da tsaro, da dai sauransu, kana kasar Sin na son hadin gwiwa da kasashen Afirka a wadannan fannoni. Daga baya, shugaban na kasar Sin ya gabatar da cikakken shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na shekaru 3 masu zuwa, wanda ya shafi fannoni 10, da suka hada da cudanyar al’adu, da cinikayya, da tsarin masana’antu, da kayayyakin more rayuwa, da aikin gona, da dai makamantansu.
Bayan da na saurari jawabin shugaba Xi, na ga jawabin ya nuna akidar Sin ta hadin gwiwa da kasashen Afirka, ta “gaskiya, da kauna, da sahihanci, gami da daukar hakikanan matakai”.
Don tabbatar da akidar, ya kamata a kula da moriyar kasashen Afirka. Hakika a cikin jawabin shugaba Xi, an ambaci dimbin matakan da za su haifar da moriya ga kasashen Afirka, misali “sanya kasashen Afirka samun karin riba bisa sarrafa kayayyaki” da “kara kwarewar kasashen Afirka wajen kiwon lafiya” da “taimakawa kasashen Afirka a kokarinsu na samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba” da dai sauransu.
Ban da haka, don aiwatar da akidar Sin a fannin hulda da kasashen Afirka, dole ne a aiwatar da matakan yadda ya kamata. A wannan fanni, za mu ga shirin da shugaba Xi Jinping ya ambata ya kunshi dimbin alkaluma, misali “ cikin shekaru 3 masu zuwa”, da “aiwatar da ayyukan hade kayayyakin more rayuwa 30”, da “tura kwararru masu ilimin aikin gona na zamani 500 zuwa nahiyar Afirka”, da “samar da akalla guraben aikin yi miliyan 1 ga mutanen Afirka”, da dai sauransu. Wadannan jimiloli an bayyana su sarai. Hakan ya nuna cewa za a iya aiwatar da matakan da aka tsara.
Sai dai watakila za ku so ku san dalilin da ya sa kasar Sin ke kula da moriyar kasashen Afirka, da neman taimakawa kasashen Afirka wajen cimma burinsu na zamanantar da kansu. Hakika jawabin shugaba Xi ya nuna dalilin da ya sa Sin yin haka, wanda ya kasance babbar manufar kasar ta fuskar hulda da kasashen waje, wato gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya.
Mene ne ma’anar manufar? Idan mutane na wasu wurare sun samu rayuwa mai wadata da kwanciyar hankali, yayin da sauran mutane suka dade suna zama cikin yanayin talauci, da yunwa, har ma da yake-yake, to, wannan rashin daidaito tabbas zai haddasa rikici tsakanin gungun mutane, da lalacewar muhallin halittu, da rashin wani daidaitaccen tsari mai amfani a fannin kula da al’amuran duniya, da dai sauransu, wadanda za su haifar da barazana ga daukacin dan Adam. Saboda haka, an ce daukacin dan Adam na da makomar bai daya. Sa’an nan raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya, na nufin sa kaimi ga hadin gwiwa don tabbatar da moriyar kowa, da neman ci gaban tattalin arziki na bai daya, tare da zummar sanya dukkan mutanen duniya samun zaman rayuwa mai inganci.
Kamar yadda shugaba Xi ya bayyana a cikin jawabinsa, “yawan al’ummar kasar Sin da ta nahiyar Afirka baki daya bisa yawan mutanen duniya, ya kai kashi daya cikin uku. Saboda haka, idan babu zamanantarwa a Sin da Afirka, ba za a samu zamanantarwar daukacin duniya ba.” Burin kasar Sin shi ne hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a kokarinsu na zamanantar da kansu, ta yadda za a iya sa kaimi ga zamanantar da daukacin kasashe masu tasowa, gami da tabbatar da ci gaban dan Adam baki daya a karshe. (Bello Wang)