• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Waraka Daga Bashin Ketare

by Sulaiman and Muktar Anwar
2 years ago
in Bakon Marubuci
0
Waraka Daga Bashin Ketare
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

An sha nanatawa cikin wannan rubutu cewa, shi bashi a kankin-kansa babu laifi don wata Kasa ta amshe shi da niyyar ta amfana ta kuma amfanar.

A nan Nijeriya, al’umar Kasa ba su dace ne ba da shugabanni masu kishin kasa da al’umarsu, wadanda suke da niyyar amsar bashi, don su amfanar da jama’ar jihohin nasu, tare da daura azamar bin hanyoyin da wadancan basuka da aka ciwo, a sanya wani asasi managarci na zahiri, wanda a fili zai tabbatar da cewa an dauko hanyar rabuwa da basukan cikin salama.

  • Tarihin Tsohon Shugaban Kasar Sudan Omar el-Bashir

Akwai hanyoyi jingim da masana da masharhanta kan ta gabatar da su a matsayin waraka, ko a kira su da cewa, sune hanyoyin salama, wajen rabuwa lafiya tsakanin mai cin-bashin, da kuma wanda aka ciwo bashin daga gare shi. Da shugabannin Afrika na yau, na da gudun afkawa tarkon irin wadancan Kasashe na yamma da ke dankara mana basuka dare da rana da mummunar manufa, to da babu bukatar gwaggwafewa tsawon kwanaki ko a ce Satika, a na ta gabza irin wadannan rubuce-rubuce. Rashin kishi da ya baiyana a zahiri daga shugabanni, musamnan irin namu na Afrika, shi ne uwa uba, wajen tashin hankulan masana da sauran masharhanta, na son ganin an ankarar da al’umar Kasa game da irin mamakon bala’in da ake fuskanta. Duk da cewa, masu ciwo irin wadancan basuka da kuma ‘yan korensu, ba su cika son a na ankarar da jama’a game da irin wannan talalabuwar da ake ciki tsundum ba. Masani ko masharhanci, bai zama mai yin wani bayani ko sharhi, da kudirin cin-fuska ko yunkurin urustawa wani ba. Idan aka sami wani cikinsu da irin wannan danyen kudiri, la-shakka bai amsa sunansa na masani, ko marubuci ko masharhanci ba!
Daga cikin hanyoyin salama ko waraka daga tarkunan tozon basukan da Kasashen Turai ke antayo mana, sun hadar da;
1- Sanya basukan a inda za su haife. 2- Amfanuwa daga mamakon arzuka da aka yi mana baiwarsu, musamnan harkar gona. 3- Dakile ta’adar cin-hanci da rashawa. 4-Inganta harkar lantarki a Kasa. 5- Samar da gungun masana masu kishin kasa a gaba, tare da neman kyawawan shawarwarinsu. 6- Rage dawainiyar tafiyar da gwamnati. 7- Samar da shugabanci nagari a matakin mazaba, karamar hukuma, jiha, da kuma uwa uba, wato matakin Kasa, da sauransu.

Amfanuwa Da Mamakon Arziki Da A Ka Yi Mana Baiwarsu
Babu shakka, mutuwar zuciya ce ta mai da jama’ar wannan Kasa tamu ta Nijeriya dogara kacokan da sabgar man fetur, a matsayin wata hanya daya tilo da za ta rika samar mana da sama da kashi tamanin ga tattalin arzikinmu na Kasa!. Hakika akwai hanyoyin arzuka iri daban daban cikin wannan Kasa, wadanda ma suka kere fetur sau ninkin ba ninki wajen bunkasar sha’anin tattalin arziki, musamnan sabgar noma, wadda wasu Shekaru can baya, ita ce kashin bayan tattalin arzikin wannan Kasa. Kuma, tun daga wancan lokaci zuwa yau din, harkar noma ce kan gaban fetur, wajen samawa dubban jama’ar Kasa aiyukan-yi.
Yankin arewacin wannan Kasa ta Nijeriya, na daga wuraren da suka fi ko’ina a Duniya kyawon kasar noma. Yankin na arewa, ya fi ko’ina a yankin Afurka ta yamma (West Africa) yawan matattarar ruwa, ko a ce dam dam, wanda ake amfani da su wajen noman rani. Ga dandazon albarkar jama’a da Allah Ya ba mu, wadanda za su wadata wajen noma irin wadannan kyawawan kassai da aka yi mana baiwarsu. Bangaren noman ne ke samawa dubban jama’ar yankin aiyukan-yi sama da komai a ban Kasa, sai dai, shugabanni sun gaza shigowa bangaren na noma, don inganta shi ingantawa.
A Kasar Amurka, Kasar da shugabanni suka shiga harkar tallafar noma kan-jiki kan karfi, ta tabbata cewa, kudin shigar da lemon zaki “Orange” kawai ke samawa Kasar a Shekara, ya fi kudin shigar da gwamnatin Nijeriya ke samu a Shekara wajen man fetur!. Ita kanta Amurkar, ba za ta fada mana ni’imar albarkatun kasa ba, amma sai ga su sun fi mu amfanarsu. Me ya sa? Amsa, shugabanninsu da gaske ne suke, a yunkurinsu na inganta tattalin arzikin Kasar.
Iskar gas kawai da Allah Yai wa Nijeriya baiwarsa, zai iya daukar nauyin bai wa daukacin nahiyar Afurka da ke kunshe da Kasashe 52 ko 53 wajen sama musu wadatacciyar iskar gas. To Amma dan Nijeriya a yau, nawa ne yake shan litar gas? Da kuma mai karatu zai lalubi wasu Kasashe cikin Duniya da ko kama kafarmu ba su yi ba wajen mallakar iskar gas din, sai ya samu kuma sun fi mu shan gas din da arha!. Wadanne irin shugabanni muke da su ne? Eh mana, tun da sarrafawa da inganta harkar gas din, na hannunsu ne.
Misali mutum ya ce fetur, gas, rake, lemo da makamantansu, za a ga an ba mu albarkatun kasa na abubuwa daidai har sama dari biyu da hamsin (250) iri daban daban. Cikin wadannan albarkatun kasa akwai bishiyar Katako, wani masani ke cewa, da Nijeriya za ta inganta bishiyoyin Katako da take da su, su kadai, za su iya zama abin dogara kamar man fetur, kuma su rike Kasar. Wane shiri ne a kasa a yau da mutanen wannan Kasa za su ce sun ga gwamnati na yi, don inganta sabgar bishiyoyin Katakonta?
Mutum ya dauki gyada kawai, zai yi matukar mamakin irin tattalin arzikin da ke kunshe cikinta. Daga gyada, akwai sinadaran da ake yin sabulu, abin yin biskit, abin yin abincin dabbobi, abincin kifi, abincin kaji da sauransu. Ka da mai karatu ya mance da man girki da ake samu daga gyadar. Ko mai karatu ya san da cewa a na yin makarin inji daga matsanancin hucin zafi, wanda a turance ake kira da “engine gasket” da bawon gyadar? To amma a yau, wane hobasa ne na hakika ba na baka ba, da za a ce gwamnatocinmu na yi, don ganin mun amfana hakikar amfanuwa daga mamakon tattalin arziki da ke kunshe cikin gyada?
Cikin wata budaddiyar wasika da Dattijo, Alhaji Dattijo Adhama ya rubuta zuwa ga hukumomi masu gudanarwa da masu yin doka na arewacin wannan kasar, “An Open Letter To The Northan Edecutibes & Legislatures” a Watan Yulin Shekarar 2021 (July, 2021), da mutum zai duba shafi na biyar (P5) na wannan wasika, zai amfana da wata irin kididdiga da aka yi, wadda ta nuna irin biliyoyin kudaden da jihar Kano za ta iya samu a kullum daga man gyadar da za a sha a cikin jihar. Cikin kididdigar, an nuna cewa, jihar ta Kano na iya samun kudin shiga sama da naira biliyan saba’in da biyu (N72b) a kullum. Da sharadin, wancan bangare na masu zartarwa da masu doka sun shigo sun gama kai wajeguda, tare da datse shigowar man gyadar daga Kasashen ketare, ta hanyar yin doka a Majalisa.
A tsakanin garin Makoda da Dambatta, akwai wani nau’in yashi da Kasar China ke ta begen ganin ta sami kai wa ga tononsa, don sana’anta gilashi da shi. Duk cikar Kasar ta China, ba su da wani ma’adin yin gilashi sama da irin wannan yashi na tsakanin Dambatta da Makoda. Idan ban manta ba, wani lokaci can baya, ta hanyar Malam Gambo, shugaban ma’aikata “Staff Officer” na Kasuwar Sabon Gari, ya gabatar min da shugabancin masu harkar gilashi ta Kasuwar Kofar Ruwa, na wuce gaba zuwa kai kuka ga Sanatan yankin, Barau Jibril”, da zimmar ya wuce musu gaba wajen tono yashin, amma lamarin ya gagari kundila.
Ba sai Kano ba, muddin mai karatu dan Nijeriya ne, ba zai gaza tunanin wani ma’adin ko albarkar Kasa da Allah Ya hore musu a yankinsu ba. Babbar matsalar a yau ita ce, masu mulki ba su damu da hako ko amfanar da jama’ar Kasa daga irin wadancan amfanoni da Allah Yai mana baiwarsu ba. Sai ma aka wayigari, idan akwai wani ma’adani a waje, sai a sami wasu marasa kishin kasa su game baki da Turawa, a zo a haddasa mummunar fitinar da za ta kai ga kashe rayukan dubban jama’a a wajen. Bayan kowa ya yi kaura ya yi gudun tsira da ransa, sai wadancan marasa kishin kasa da bakin haure su dukufa kwasar wadancan ma’adanai, shin, me ke faruwa a Zamfara a yau?
Duk irin albarkatun kasa da aka yi wa wata Kasa baiwarsa a Duniya, muddin shugabanninta ba sa kishinta, to fa a banza, ba za su amfana ba. Kuma ba za a bar su su zauna lafiya ba.
Da shugabanni a Nijeriya za su karkata ga sabgar noma kadai, su zuba jari ciki, su samawa manoman taki da kasuwa, babu shakka da an fita daga wannan kagaggen talaucin da aka jefa jama’ar wannan Kasa ciki. Talaucin Kasar Nijeriya ba daga ne yake ba, tun da Allahn Ya ba da mafita.

Samar Da Gungun Masana Masu Kishin Kasa
Dole ne gwamnati ta yi zabarin manyan mutane masana gogaggu, wadanda lamarin Kasar ne ke kunshe cikin zukatansu sabanin muradansu na son zuciya. Hakika Allah Yai mana baiwar mutane hazikai masana, wadanda hatta sassan Kasashen Duniya ke daukarsu aikin dindindin da na kwantaragi, don inganta harkokin Kasashen nasu. Dole ne a lalube su, a saurari shawarwarinsu, a dabbaka abubuwan da za su gabatar a matsayin shawara ko a matsayin wani sharadin da wajibi ne binsa, wajen inganta harkokin tattalin arzikin namu, muddin a na son A’i ta fita daga rogo ba tare da ta karce jiki ba.
Lokacin da marigayi Umar Musa ‘yar’adua ya tasamma yin gyara game da sha’anin Zabe a Nijeriya, ya kafa wani babban Kwamiti ne a karkashin tsohon babban Joji na Kasa Uwaisu, da sauran masu kishin kasa, mutane irinsu Farfesa Attahiru Muhammad Jega, OFR, ai sanin kowane cewa, a karshe, laya ta yi kyawon rufi. Gwamnati ba ta yi wa kwamitin wani katsa-landan ba, sannan kuma ta tasamma dabbaka irin shawarwarin da wancan kwamitin ya gabatar mata. Bugu da kari, gwamnati ta dauko guda daga cikin ‘yan kwamitin, Jega, ta danka hukumar zaben Kasar kacokan a hannunsa, hakan ne ya jaza aiwatar da zabukan da ba a taba samun masu ingancinsu ba cikin tarihin Zabukan Kasar gabaninsu, wato Zabukan Shekarun 2011 da na 2015, kamar yadda masana da sauran masu sanya idanu na gida da waje suka fadi.
Ko da an kafa wani kwamiti na masana kuma masu kishin kasar, muddin za a yi musu katsa-landan cikin sabgar kwamitin, ko kuwa, shawarwarin da suka gabatar, a yi wurgi da su, to fa babu inda za a je, sai dai kawai a ci gaba ne da tsalle a wajeguda kamar yadda aka saba.
Duk kyawon wani kwamiti da sunan gyara tattalin arzikin Kasa da aka kafa, ko za a kafa ba bisa cikakkiyar cancanta ba, shi ma ba zai cimma komai ba mai alfanu, lamura za su ci gaba da wakana ne cikin yanayi na daben-kwalo.
Duk karatu da Dr Abel Guobadia da Professor Maurice Iwu ke da, ba su jagorantar Hukumar Zabe, INEC, ta Kasa da aka yi bisa wata manufa, a karshen lamarin, sun gudanar da wasu nau’ikan Zabuka ne gurbatattu, wadanda gabaninsu a Kasar, ba a taba cin karo da miyagun Zabukan irinsu ba!.
An sha gani a Kasar, inda ake shugabantar da wadanda ba su cancanta ba kawai bisa wasu dalilai na siyasa, ko na ‘yan’uwantaka, ko na abokantaka, ko na iyalantaka da sauransu, a karshe ai kwalliya ba ta biyan kudin sabulu ne. Misali, irin gwamnatin Mai-barin Gado Mr Clean.
A sati mai zuwa za mu karkare wannan batu na BASHIN GIDA DA NA KETARE IN SHA ALLAH!

Labarai Masu Nasaba

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?

Waraka Daga Bashin Ketare


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Matawalle Ya Gwangwaje Jama’ar Zamfara Da Rabon Shanu Da Ragunan Layya

Next Post

Cikin Alhazan Nijeriya An Samu Masu Larurar Kwakwalwa Da Masu Juna Biyu

Related

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?
Bakon Marubuci

Ta Ya Ake Gudanar Da Nagartacciyar Rayuwa?

4 weeks ago
Waraka Daga Bashin Ketare
Bakon Marubuci

Waraka Daga Bashin Ketare

1 month ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [21]

2 months ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20]

2 months ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [19]

2 months ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
Addini

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18]

2 months ago
Next Post
Cikin Alhazan Nijeriya An Samu Masu Larurar Kwakwalwa Da Masu Juna Biyu

Cikin Alhazan Nijeriya An Samu Masu Larurar Kwakwalwa Da Masu Juna Biyu

LABARAI MASU NASABA

ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

May 15, 2025
‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

May 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

May 15, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa

May 15, 2025
UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.