A yau Argentina za ta fafata da Faransa a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ranar Lahadi da Qatar ke karbar bakunci.
Tambayar da kowa yake yi shine ko dan wasa Messi zai dauki Kofin Duniya na farko a tarihin rayuwar sa, ko kuwa Mbappe zai lashe na biyu a jere a karawar da za su buga da misalin karfe 4 a filin wasa na Lusail.
Messi, wanda yake buga wasa a PSG mai shekara 35, ya lashe gasar Ballon d’Or bakwai da Copa America da sauran kofuna da yawa, amma bai taba daukar na Duniya ba.
Argentina ta lashe Kofin Duniya biyu jumulla, amma rabon ta da lashe kofin tun 1986 karkashin jagorancin marigayi Diego Maradona.
Wannan karawar za’a yi tsakanin ‘yan kwallon Paris St Germain da suke buga wasa tare, wato Messi da Kylian Mbappe.
‘Yan wasan biyu na takarar lashe kyautar takalmin zinare a matakin, wanda ke kan gaba a cin kwallaye a Gasar, kowanne yana da biyar-biyar a raga a Qatar.
Yayin da Olivier Giroud na Fransa da dan kwallon Argentina, Julian Alvarez kowanne yana da hur-hudu a raga.
Messi ya ja ragamar Argentina kai wa wasan karshe a Gasar Kofin Duniya a 2014, amma Jamus ta doke su 1-0 a Brazil, bayan karin lokaci, Mario Gotze ne ya ci kwallon.
A tarihi Argentina ta lashe kofin Duniya guda biyu na farko a gida a 1978, sannan a 1986 a kasar Mexico.
Faransa ma guda biyu ne da ita, wadda ta fara dauka a gida a 1998, sannan ta lashe a 2018 a Rasha.
Kowacce na fatan daukar na uku jumulla, sai dai Fransa na sa ran daukar na biyu a jere bayan bajintar da Brazil ta yi a 1962 – sai dai Italiya ce ta kafa tarihin cin biyu a jere a 1934 da kuma a 1938.
Kasashen biyu sun kece raini sau uku a Gasar Kofin Duniya, inda Argentina ta yi nasara a fafatawar cikin rukuni a 1930 da kuma 1978 – sai dai Faransa ce ta ci Argentina 4-3 a zagayen siri daya kwale a 2018.
Argentina za ta buga wasan karshe na shida a Gasar Kofin Duniya, Jamus ce kan gaba a yawan kai wa fafatawar karshe inda ta buga guda takwas.
Argentina ta dauki Kofin a 1978 da 1986, sannan aka doke ta a karawar karshe a 1930 da 1990 da kuma 2014.
Watakila Argentina ta zama ta biyu da ta yi rashin nasara a wasan farko a Kofin Duniya, sannan ta lashe Gasar kamar yadda Sifaniya ta yi a 2010.
Haka kuma kila Messi ya zama na uku daga Argentina da zai lashe takalmin zinare, bayan Guillermo Stabile a 1930 da kuma Mario Kempes a 1978.
Faransa ta halarci karawar karshe a Gasar Kofin Duniya karo na hudu.
Faransa na fatan zama ta uku da za ta lashe Kofin Duniya biyu a jere, bayan Italiya a 1934 da 1938 da kuma Brazil 1958 da 1962.
‘Yan Wasan Faransa Basu da lafiya
Yan wasan Faransa da dama sun kamu da sanyi a sansaninsu da ke Doha gabanin wasan na karshe.
Na baya bayannan sune masu tsaron baya Raphael Varane da Ibrahim Kounate, wadanda rashin lafiyar ta hana su yin atisaye.
Dama mai tsaron baya Dayot Upamecano da dan wasan tsakiya Adrien Rabiot ba su samu buga wasan kusa da karshe ba da Faransa ta yi nasara kan Maroko.
Kasar Qatar ta kafa tarihi
Kamar yadda shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino ya bayyana, Qatar ta yi nasarar shirya gasar cin kofin duniya da tarihi ba zai taba mantawa da ita ba.
A cewar sa, duka kasashen da suka samu halartar gasar sun bar Qatar da ke Gabas ta Tsakiya da wani abun alkhairi da ba zasu taba mantawa ba.
To amma babban abunda yafi jan hankali a hirar da ya yi da manema labarai shi ne, batun sauya gasar kofin duniya daga kasashe 32 zuwa 48.
Kuma za’a fara aiwatar da hakan ne a gasar ta gaba, ta hadaka tsakanin kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico a 2026.
Ana tunanin samar da rukuni 16 mai kasashe uku-uku, ko kuma rukuni 12 mai kasashe hudu-hudu.
A karkashin sabon tsarin nahiyoyi za su samu karin kason kasashen da za su wakilce su, inda ake hasashen Afrika za ta samu karin kasashe daga biyar zuwa tara.
Za kuma a fadada gasar kungiyoyin duniya 32, da zasu buga tsakaninsu a gasar da ya kira FIFA Club World Cup ta maza da ta mata.
A gasar France 98 ce FIFA ta fadada gasar kofin duniya zuwa 32.
Wanene alkalin wasan da zai jagoranci wasan na karshe?
Tuni dai kwamitin da ke jagorancin alkalan hukumar kwallon kafa ta duniya, ya zabi Szymon Marciniak a matsayin wanda zai jagoranci wasan na karshe tsakanin Faransa da Argentina.
Marciniak, dan kasar Poland mai shekaru 41 a duniya na cikin tawagar alkalan da suka jagorancin wasannin kasashen biyu kafin a kawo wannan mataki na wasan karshe.
Akwai wasan da Argentina ta doke Australia a zagayen kwaf daya, da kuma wanda Faransa ta doke Denmark a wasan rukuni duka shine ya jagoranci wasannin.
A ranar Alhamis ne FIFA ta sanar da sunansa a matsayin wanda zai raba gardama, a wasan da duniya ke dakon gani tuntuni.
Ana yi wa Szymon Marciniak kallon alkalin wasa mafi shahara a Poland da ma daukacin Turai, kuma kwarewarsa tasa hukumar kwallon kafar Turai ta bashi alkalancin wasan karshe na Uefa Super Cup.
Kazalika FIFA ta bayyana sunayen Pawel Sokolnicki da Tomasz Listkiewicz, wadanda dukansu suma yan Poland ne, a matsayin masu taimaka masa.
A al’ada a kan bai wa tawagar masu alkalanci zinariya kafin bada kofi ga kasar da ta yi nasara.