Connect with us

WASANNI

Wasanmu Da Argentina Kamar Yaki Ne, Cewar Ighalo

Published

on

Dan wasan gaba na tawagar Super Eagles, Idion Ighalo ya bayyana cewa wasan da Nijeriya zata fafata da kasar Argentina kamar yaki ne a kokarin da kowacce kasa takeyi na ganin ta samu nasara domin kaiwa mataki na gaba a gasar.
Acikin rukunin dai kasashe uku da suka hada da Nijeriya da Argentina da kuma Iceland kowacce kasa zata iya kaiwa mataki na gaba idan har tasamu nasara a wasanta na gaba da za’a fafata a yau Talata a wasa na uku kuma na karshe a rukunin.
Nijeriya dai tana mataki na biyu yayinda take da tazarar maki biyu tsakaninta da kasashen Argentina da Iceland bayan da kasar Crotia tuni ta samu tikitin zuwa mataki na gaba bayan ta samu nasara akan kasashen Nijeriya da Argentina.
“Argentina zata fito neman cin wasa kuma za subi duk wata hanya da suka san anabi domin suci wasa saboda haka wasan kamar yaki ne ko kuma wasan karshe amma nasan cewa duk munada nasara akansu” in ji Ighalo
Ya kara da cewa yasan yan wasan Super Eagles suma a shirye suke da wasan kuma sun shirya tsaf domin tun karar wasan da Argentina saboda kowa yasan Argentina babbar kasace kuma suma ba kanwar lasa bace.
Argentina da Nijeriya dai sun hadu sau hudu a gasar cin kofin duniya a tarihi sai dai har yanzu Nijeriya bata taba samun nasara ba a haduwar gaba daya.
Advertisement

labarai