A ranar biyu ga watan Yuli aka fara gasar kwallon kafar mata a gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasar Morocco za ta karbi bakunci, wadda ake kira Women’s Africa Cup of Nations (WAFCON).
Nijeriya kasar da ta lashe gasar a baya, ta tafi da ‘yar wasa Asisat Oshoala da Ashleigh Plumptre cikin tawagarta da ta halarci gasar, sai dai kociyan tawagar Randy Waldrum, ya cire sunan ‘yan wasa Gift Monday da Ngozi Okobi-Okeoghene daga tawagarsa.
Sai dai farko tun da hukumar kwallon kafar kasar ta NFF ta shiga tsaka mai wuya lokacin da take son rage sunayen yan kwallon daga 32 zuwa 28 da za a halarci gasar da su, kawo yanzu ‘yan wasan Nijeriya 28 da za su wakilci Nijeriyar a wannan babbar gasa, suna Moroko domin buga gasar kuma tuni su ka yi rashin nasara a wasan farko da ci 2-1 hannun ‘yan wasan kasar Afirka ta Kudu.
An fara gasar Afirka ta mata ta WAFCON 2022 a ranar 2 ga watan Yuli zuwa 23 , kuma za a yi gasar a Moroko sannan tawagar Nijeriya da ake kira Super Falcons ta fafata da Bayana-Bayana ta Afrika ta Kudu a ranar 4 ga watan Yuli a matakin rukunin C sai sauran kasashe biyun da ke cikin wannan rukuni sun hada da Burundi da Botswana.
Kasashe 12 ne za su buga wannan gasa wadda za ta gudana a Morocco. Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF ta rarraba kasashen zuwa rukuni uku dauke da kasashe hudu kowanne kamar yadda aka saba.
Rukunin A:
Morocco da Burkina Faso da Senegal da kuma Uganda.
Rukunin B:
Kamaru da Zambia da Tunisia da kuma Togo sai
Rukunin C: Nijeriya da Afirka ta Kudu da Burundi da kuma Botswana.
A shekarar 2021 ba a samu damar gudanar da wannan gasa ba saboda annobar Korona, kuma gasar da za ta gudana a Arewacin Africa, ita ce ta farko da aka buga daga kasashe 8 zuwa 12.
Kamar ko wacce irin gasa, akan samun kasashen da suke halartar a karon farko a wannan shekarar ma an samu wasu kasashen guda hudu da suka zo a karon farko da suka hada da Togo da Burundi da Burkina Faso da kuma Botswana.
Kasar da ke kan gaba cikin jerin kasashe ita ce Nijeriya, Super Falcons kuma na daya a kungiyoyin Afrika ta 39 a duniya kuma gasa uku ta baya da ta gudana Nijeriya ce ta lashe, kuma karo tara da ta lashe a jumulla.
‘Yar wasanta mai buga wasa a Barcelona Assisat Oshola ita ce ta fi kowacce buga wasa a gasar, sannan ita ce ta lashe takalmin zinare a babbar gasar kwallo ta mata ta Sifaniya kuma ta ci kwallo 20 cikin wasa 19 da ta buga, kuma an ba ta kyautar ne tare da ‘yar kasar Brazil Geyse Ferreira wadda ta ci kwallo 20 a wasanni 27 da ta yi.
Kasashe hudu da za su kai karawar dab da na karshe a gasar kofin Afirka ta bana, su ne za su wakilci Afirka a gasar kofin duniya ta mata da za a yi a shekarar 2023, sai sauran kungiyoyin biyu za su yi wasan samun gurbi ne da za a fafata tsakanin kasashen 10 domin halartar kofin duniya da za a yi a kasashen Australia da New Zealand.