Wasikun Obasanjo!

Cigaban fasaha ya kawo canji a rayuwarmu ta kowacce fuska kama daga tattalin arziki, ilimi da tsaro. Hanyoyin sadarwa na zamani a nan Nigeria sun zama hanyoyi da ake yada labarun karya wadanda ke kara kawo rarrabuwar kawunan al’ummomi. Babban abin takaici shi ne lalacin mu na gazawa wajen tantance labarai na karya kafinmu yada su.

Shekaru 1400 da su ka wuce, cikin umarnin Allah wanda ba ka ganin irinsa a tsarin koyarwa na harkokin yada labarai a makarantun koyar da jarida shine umarnin cewa K17:36: “Kuma ka da ka bi (yarda da) abinda ba ka da ilimi game da shi. Lallai ne ji da gani da zuciya da allah ya baku, za a tambaye ku a kansu.”

Wannan aya ita ce ginshiki a game da duk wani bayani da ya iso gareka a rayuwa. Ka da ka bi wani abu cikin jahilci sai ka sami ilimi game da abun. Idan kowa ya dauki wannan dabi’a, hakan zai dakile yada duk wani labari na karya. Sannan Allah ya sake cewa cikin K49:6 “Ya ku wadanda ku ka yi imani! Idan wani fasiki ya zo muku da  wani Babban labari, to ku nemi bayani domin ka da ku cuci wadansu mutane a cikin jahilci.”

Wato tun zamanin annabi wannan aya ta yi gargadi a kan labaran karya (fake news) tare da jan hankalin cewa kafin ku yarda har ma ku yada wani labara, wajibi ku fara bincika ku tabbatar da sahihancin labarin. Wadannan ayoyi guda biyu su ya kamata su zama mana jigon mu’amalarmu da ta shafi kowanne fanni na labarai da bayanai, domin za su ba mu gaskiyar bayanai da kuma kaucewa daga labaran karya.

Idan mu ka koma kan wasikun Obasanjo, duk ta yadda ka ke kallonsu da irin sikelin da ka dora su, hakika sun kasance masu tasirin gaske wajen yadda tarihin siyasa da mulki na tsawon shekaru 40 a kasar nan ya kasance.

Obasanjo ya fara rubuta irin wannan wasika tun a zamanin mulkin Shagari, inda bayan rantsar da gwamnatin a karo na biyu a shekarar 1983 ya fito ya caccaki yadda a ke mulkin kasar ta yadda yan siyasa su ka gaza a harkar tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa. ’Yan makonni kalilan da wannan suka ta Obasanjo, sojoji su ka kifar da gwamnatin tare da dakatar da mulkin dimokuradiya.

Shekaru goma bayan wannan juyin mulki, a shekarar 1993 sai gwamnatin IBB ta soke zaben shugaban kasa wanda ake ganin Moshood Abiola ya lashe. Wannan ya kara wa Obasanjo kaimi wajen sukar gwamnatin Babangida wanda dole a karshe ya aje mulki tare da kafa gwamnatin rikon kwarya.

Sukar Obasanjo ta ta’azzara a lokacin mulkin Abacha domin a taron da aka yi a Arewa House ya zargi gwamnatin da cewa ba ta san ina ta sa gaba ba. Bayan nan ya sake yin hira da BBC inda ya fito karara ya zargi gwamnatin Abacha da cin hanci da rashawa tare da almubazzaranci da dukiyar kasa. Saidai sabanin IBB da ya yi kunnen-uwar-shegu da Obasanjo, Abacha ya sa an garkame shi a kurkuku tare da cajinsa da hannu a kokarin juyin mulki. Obasanjo bai fito daga kurkuku ba sai bayan mutuwar Abacha.

Obasanjo ya sami darewa kujerar mulkin Nigeria a karo na biyu a matsayin farar hula a 1999, lokaci na farko da bai rubuta wasika ko caccakar gwamnati ba, sai dai kokarin tazarce da ya yi wanda bai kai ga nasara ba.

Dan takararsa da ya zaba a 2007, Umaru Musa Yar’Adua ya lashe zabe amma cikin dan kankanen lokaci Obasanjo ya fara sukar gwamnatinsa. Yar’Adua bai dade ba ya rasu inda Jonathan ya gaje shi.

Mai hali baya barin halinsa, Obasanjo ya ci gaba da sukar Jonathan tsawon shekaru shida da ya yi mulki. Wasikarsa ta karshe da ta kunshi abubuwa guda 10, ciki har da gargadin Jonathan kada ya tsaya takara a 2015. Bayan ya yaga katinsa na dan jam’iyyar PDP tare da fitowa fili ya goya wa Buhari baya, mulkin PDP na shekaru 16 ya zo karshe.

Kamar yadda ya saba kafin shekaru hudu na karon farkon mulkin Buhari ya rubuta masa takarda amma sai dai kash! A karon farko wasikar Obasanjo ba ta yi tasiri ba wajen kifar da gwamnati domin yan Nigeria sun sake zaben Buhari a karo na biyu a zaben 2019.

Wannan ya kawo mu kan wasikar Obasanjo ta karshe wadda ya saki a wannan sati. Wannan wasika ta sha banban da irin wasikun da ya saki a baya saboda dalilai da dama. Na farko dai ya saketa ba kusa da lokacin zabe ba kamar yadda ya saba, sannan kuma kalamansa ba irin wadanda ya saba a baya ba da ke cike da izza da bani-na-iya.

Sannan ya fito da mahimman abubuwa da duk mai kishin Nigeria ya kamata ya tsaya ya dubi abubuwan da zummar yadda za’a samar da mafita. Kasancewar idanuwa sun rufe da gaba da juna ya sa mutane da dama ba sa ganin irin hadarin da Obasanjo ke jawo hankali a kai.

A cikin wasikar Obasanjo ya ce “…a na yada bayanai da ba gaskiya ko kuma labaran karya” kuma kamar yadda mu ka sani wannan gaskiya ce kuma hanya mafi hadari da ake amfani wajen tunzura wutar kabilanci da bangaranci da addini.

Kada mu manta irin wannan hanya a ka yi amfani da ita a shekarun 1994 inda mutanen Hutu su ka rika kiran yan Tutsi kyankyaso kuma a ka yi musu kisan kiyashi da ba’a taba ganin irinsa ba kawo wannan lokaci, inda mutane tsakanin 800,000 zuwa miliyan daya su ka hallaka a kwanaki 90. A yau kafafen sada zumunta na Nigeria cike su ke da maganar yan ta’addar Fulani ana furofaganda iri-iri wadda ke harzuka mutane.

Abin tambaya shine ya aka yi Fulani su ka sami kansu a wannan matsayi? A wasikarsa Obasanjo ya yi kokarin amsawa inda ya ce “Rikon sakainar kashi da gwamnati ta yi game da rikicin makiyaya da manoma ya watsu inda ya juye zuwa ta’addanci, satar mutane, fashi da makami da kisan kai a fadin kasar nan.”

Idan mu ka dubi matsalar za mu ga cewa maganar Obasanjo gaskiya ne domin zuba ido da mu ka yi a kan rikicin manoma da makiyaya ya sa an rika kashe Fulani da dabbobinsu ta yadda yawanci wadanda su ka shiga wadancan munanan halaye sun sami kansu a matsayin an kashe musu yan uwa da dabbobi kuma an kona muhallansu. Yawancin wadannan Fulani da ke satar mutane sun shiga ne saboda neman fansa da kuma rashin madogara a rayuwarsu.

Duk da wadannan dalilai shin adalci ne a gurinmu wajen goyon bayan Fulani don kawai su yan uwanmu ne? shin a cikin ta’addancin da wadannan Fulani ke aiwatarwa ba mu muka fi kowa shan azabarsa ba? Ko a satin da ya gabata a jihar Katsina wadannan yan ta’adda sun farma garin Kirtawa da ke karamar hukumar Safana da rana sun karkashe mutane da dama.

Mutanen garin sun kasance idan dare ya yi mazajen garin su kan gudu zuwa makwabtan kauyuka su kwana sai da safe su dawo, wannan ya sa maharan su ka bari sai da rana su ka kawo farmaki garin lokacin da mazajen su ke nan.

Da rana tsaka ana tare hanyoyi a harbi mutane a kuma sace su sai an biya kudin fansa kuma mafi yawan wadannan mahara hujjoji sun tabbatar da cewa Fulani ne. Shin duk wanda ya ce a tashi tsaye a yi maganin wannan abin kamar yadda Obasanjo ya nema, sai ya zama aibu? Sai mu rufe ido mu na gani rayuwarmu da ta yayanmu na shiga hadari da ba wanda ya san inda zai tsaya?

Allah ya umarce mu cikin K4:135 “Ya ku wadanda su ka yi imani ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah kuma ko da a kanku ne ko a kan mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko da kuwa wanda a ke yiwa shaida ya kasance mawadaci ko matalauci.” Wannan aya ita ce ginshikin adalci da Musulunci ya koyar amma ba ma amfani da ita cikin mu’amalarmu saboda son kai ko kokarin kare wata dangantaka.

Hakika Obasanjo na cikin wadanda su ka kassara kasar nan, musamman arewa amma hakan ba zai hana mu idan ya fadi gaskiya mu goya masa baya ba. Ko shaidan ne ya zo da gaskiya wajibi a bi ta domin ba shaidan aka bi ba, gaskiyar a ka bi. Arewa na rugujewa a gaban mu duk da cewa mun fi kowa yawan jama’a, fadin kasa da albarkatu irir-iri, amma sai ga shi mune a baya wajen talauci da jahilci.

Sannan sannu a hankali muna zama wadanda basa iya gaya wa kansu gaskiya ballantana wani daga waje ya gaya musu. Idan mu na son fita daga yanayin da muka tsinci kanmu wajibi mu yarda da gaya wa kanmu gaskiya da kuma karbar ta daga duk inda ta zo mana, maimakon buya a bayan bangaranci ko addini mu rika kallon cewa ana nunawa Fulani tsana a kasar.

Mu tashi tsaye wajen kawo mafita, wadda kuma muna da ita amma mun kasa amfanar ta. Jihohin Kano da Katsina kawai na da albarkatun ruwan da idan an yi amfani da su babu dalilin da wani bafillace zai tsallaka kudu domin neman ruwa ko ciyawa. Amma duk da cewa Bafulatani ke mulki, mun kasa zartar da tsarin ruga wanda zai taimaki, ba Fulani kawai ba har al’ummar kasar.

A gaban mu Obasanjo ya sahalewa yankin Niger Delta a lokacin mulkinsa su ka sami gwaggwaban kaso 13% a arzikin kasa a lokacin da majalisa ke da rinjayen yan arewa, amma mun kasa zartar da tsarin ruga. Kamar yadda yadda shata ke cewa “Yan arewa mu bar barci..” wajibi mu farka daga wannan barci mu tashi tsaye wajen bin hanyoyi na gaskiya da za su tserar da mu ba babatu ba.

Exit mobile version