Connect with us

ADABI

Wasu Alakokin Nijeriya Ta Arewa Da Nijar Ta Fuskar Tarihi

Published

on

Babu shakka bincike ya nuna cewa ma fi yawancin jama’ar da su ka yi iyaka da Kasar Nijar da ke zaune a Nijeriya duk daga can Nijar din su ka yo kaura.Tun kafin bayyanar Shehu Usman Bin Fodiyo kakannin mu da iyayen mu su ka yi wannan kaura daga can zuwa sassan arewacin Nijeriya. Saboda ma wasu sun zama ‘yan gida, wasu sun zama saraki wasu kuma sun yi arziki a nan Niferiya, bas u so a ce daga can su ka fito. Wasu kuma bayi ne, saye su aka yi a kasuwannin da ke kan iyakokin kasashen biyu. Wasu kuma bayi ne da aka kamo lokacin yaki. Daga baya sai iyayen gidan nasu su ‘yanta su, su yi masu aure ko ma su aura masu ‘ya’yan su, su kuma su yi zuriya. Alal misali, akwai bayi da dama da Sarkin Pauwa Nuhu Nadabo (1910-1943) ya kamo lokacin ya na Kanwan Katsina, kafin, da kuma cikin zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko mai Turawa (1906-1944) Wasu bayin ya zauna da su Katsina wasu kuma ya zauna da su Kankara, kuma duk daga yankunan Maradi ya kamo su.
Musamman lokacin da Umaru Dallaje ya amso tuta daga wajen Malam Bello (da Shehu Dan Fodiyo ya tura su, su uku: da shi da Umaru Na-Alhaji da Umaru Dunyawa bayan sun kammala karatu da hudubobi) cikin 1907, a Katsina fada ya kaure a tsakaninsu da Sarkin Katsina na wannan lokacin, Magajin Haladu (1806-1807) wanda jikan Sarkin Katsina Tsaga Rana ne. Kafin Dallaje ya darkako Katsina cikin 1805, Maremawa shi ne Sarkin Katsina. Da ya ga rigima na tafe tana neman haye masa sai ya dora Magajin Haladu kanensa akan karagar mulki, shi kuma ya ari takalman kutiri ya kara gaba don yana ganin yakin za ya iya cin sa. Da ya gudu ya tafi Maradi, shi kuma sai ya koro Hakiminsa na can (a lokacin Maradi na karkashin ikon Katsina. Lokacin da Hakiminya iso Katsina sai ya tarar har Umarun Dallaje ya kafa tuta ya zama Sarki, ya yi mubaya’a ya fadi abin da ya faru. Sai aka bas hi sarautar Kurfi. Mafari ake ce masa Maradin Katsina, kuma har yau din nan zuriyar su ne ke da ikon kasar Kurfi. Shi kuma Magajin Haladu, a kan layin sa ne aka samu zuriyar su Rauda uban AbdulRahman Danbaskore (1835-1878) dukansu sun yi sarautar Maradi, har a yau din nan akwai Sarki Buzu da Sarki Ali Zaki Sarakunan Maradi, duk zuriya daya ne. To ko banza akwai alaka ta auratayya a tsakani.
Sai kwanan nan na binciko cewa kuma ashe mutanen Filinge ta Kasar Nijar din dai cewa asalin su mutanen Kurfi sne, daga can suka yi hijira su ka koma can Filinge din, duk a tsakanin wannan lokaci da Umarun Dallaje ya kori Magajin Haladu. Asalin sunan Filinge din ya taso ne daga wata mata daga cikin zuriyar mutanen Kurfi mai suna Igge, kasancewar su Fulani, dama daga su fuani ake samun sunan Igge. To a can inda Filinge din ta ke a yau, ita Igge ta share wani babban fili, ta ce nata ne, nan ta yi sansanin ta ta tsugunna. Lokacin da Turawan Faransa su ka je don shata iyakoki da rabon kasa kusan a tsakanin 1835 sai su ka ce ma su ‘wannan filin fa na wanene?’ Sai Kurfawa suka ce ma su ‘filin Igge ne’, To da su ka tashi rubutawa sai suka sanya ‘Filinge’tunda su ba Hausawa ba ne.
Hakazalika ma mutanen Dogon Dutse (kilomita 117 daga Kwanni, kuma kilomita 300 daga Yamai) asalin su mutanen Daura ne. Don hakane ma za ka iya ganin su da tsage akan kumatu irin na mutanen Daura. Nan kuma abin da ya faru shi ne Sarkin Daura na wani lokaci ya kai ziyara can (saboda a wancan lokaci ikon Kasar Daura ya kai har Agadas) sai aka ba shi diya ya aura. To dan da su ka haifa ne aka yi ma tsaga irin ta Daurawa. Shi ne ya girma ya zuba zuriya. Hakazalika kuma sai wasu daga Daura suka yi hijira suka koma can da zama. A yau, duk mutumin Dogn Dutse, da ka taba shi za ka ga cewa ya na da alaka da Daura. Za ma ka iya gane kamannin su daya, fasalin su daya, irin yanayin maganar su daya. Mutumin Dogon Dutse na da wauta da son wasa da dariya, to Badauri ma haka.
Yamai ta kasance babban birnin Kasar Nijar bayan Turawan mulkin Faransa sun amshe daga Damagaran. Asalin sunan Yamai ai zabarmanci ne, ya na nufin ‘Nya me’. Abin da ‘Nya’ ke nufi shi ne ‘bakin ruwa’, ‘me’ kuma na nufin ‘uwa ko mahaifiya’. Watau yanda abin ya faru shi ne suma mutanen Yamai asalin su daga kasar Katsina su ka yi hijira su ka koma can, amma tarihi bai nuna ainihin ko daga wanne sashe na Kasar Katsinar ba. Wadannan rigingimu da yake-yake a Katsina su ka tilasta wasu al’ummomi su ka rika gudu zuwa arwacin Katsinar wada ya hada da Yamai da makwabtan ta. To daga cikin su akwai wata mata da ta shata wata babbar iyaka gab da tekun Yamai din, nan ta ke wanka. Don haka idan za ta yi wanka sai ‘ya’yanta su sa Katanga ko shamaki don kada a gan ta. Nan mada Turawa su ka je don shata iyakoki da fidda kasa-kasa, sai su ka nemi minene sunan wannan wuri nab akin teku. Sai aka rasa sunan da za a sanya ma wurin, illa aka ce a sanya masa Nya me (ikon wannan mata tnda wurin ta ne) To daga Nyame kalmar zabarmanci, sai Hausa ta kwace zuwa Niyame ko Yamai saboda Hausa sarkin mamaya ce.
Amma matsalolin da aka samu game da rubuta tarihin Kasar Nijar da yanda aka yi wasu daga Nijeiya su ka yi kaura zuwa can shi ne ma fi yawancin malaman tarihin su ba su himmatu sosai wajen binciko tarihin garuruwan su kamar yanda namu masana da manazarta tarihin su ke yi ba. Duk da ya ke dai muma nan muna da dan tsaiko, amma mun fi su hobbasa. Akwai marubuta da mabincika a Kasar Nijar da su ka yi fice kamar su Farfesa Umaru Dankousou wanda ya a rubuta tarihin sarakunan Kasar Katsina da Sanusi Jaku, wani mutum mai ilimi da sanin tarihi, da kuma Bin Umar. Jaku ya sha rike manyan mukamai a Kasar Nijar, a ciki har da shugaban Cibiyar Kawance ta Nijeriya da Nijar (Nigeria-Niger Commission) Shi kuma Bin Umar ya taba rike mukamin mai magana da yawun Shugaba Tandja, daga bisani har ya zuwa 2013 yana rike da mukamin mataimakin shugaban majalissar dokoki ta Kasar Nijar.
Abin takaici shi ne ga su da tarin ilimi da sanin tarihi amma ba su mayar da hakullan su wajen wallafa tarihin garuruwan Nijar da mafarin su ba.
Mu na fata masana tarihi na kasashen guda biyu za su himmatu wajen zakulo musabbaban kafa garuruwa da kamanceceniya ta halayya, al’adu, da tabi’o’I na mutanen mu.
An samo wadannan tarihai daga Yamai, a wajen Alhaji Abdullahi Yamai sarkin tarihi da kuma Bin Umar, mataimakin shugaban majalissar dokoki ta Nijar, a lokacin ziyarar mu Yamai cikin 2013 da 2015.
Mu kwana nan.
Advertisement

labarai