Mairo Muhammad Mudi" />

Wasu Fa’idoji A Kan Namjin Goro Da Maganin Harbin Kunama

Namjin Goro

Assalamu alaikum masu karatu. Yau dai zan kawo maku abubbuwan da na ji daga wasu masana wanda nike ganin zai iya amfanar da mu. Kun san an ce taba-kidi, taba karatu, yau kama za mu tabi abin da ya shafi lafiyarmu ne. Allah Ya sa mu amfana, amin.

Na farko kan cizon kunama ne.

Maganin Harbin Kunama Cikin Addu’a.

Tabbas al’umma na cikin dimuwa a lokacin da kunama ta harbi wani dan’uwansu ko ta harbi mutum karan kanshi.

Wasu na kokarin su tafi asibiti wasu kuma sai dai a daure wajen da ta harba din.

Duk wanda kunama ta harbe shi ko ta harbi wani nashi to ya samu ruwa ya zuba gishiri a ciki sai ya karanta Suratul Ikhlas da Falak da Nasi sai ya tofa a cikin ruwan, idan a hannu ne sai ya sa hannun cikin ruwan idan ya kai wasu mintuna zai ji ya samu waraka da yardar Allah.

Wannan daga wurin wani mai yawan bibiyan rubutu na ne,  Usman Ahmad Mairatata. Duk mai son in hada shi da shi ya tuntube ni. Ga gudumawarsa kan namijin goron.

 

2.NAMIJIN GORO DA AMFANONIN SA GA LAFIYAR DAN-ADAM.

 

(1) YANA KASHE DAFIN MACIJI DA KUNAMA:

Namijin goro yana kashe dafin cizon maciji, idan maciji ya ciji mutum to a bashi namijin goro guda daya ya ci, insha’Allahu nan take zai kashe dafin cizon macijin.

 

(2) YANA KASHE MACIJI:

Ana shanya namijin goro ya bushe sai a daka, a barbada a wajen da ba a so macijin ya shiga, idan macijin ya ketara wannan garin namijin goron to nan take zai mutu.

 

(3) YANA KASHE GUBA:

Duk wanda ya sha wata guba da gan-gan ko bisa kuskure, a basu namijin goro kwara daya ya cinye, insha’Allah zai amayar da gubar da ya sha.

 

(4)YANA FITAR DA DUK WANI CUTA:

Ana yayyanka namijin goro a jika a rika sha, insha’Allah duk wata gubar da ke jikin mutum za ta fita.

 

(5)YANA KARA KARFI:

Ana cin namijin goro saboda da karin karfi ga masu iyalai ‘yan mintuna Karin a je ga iyalan.

 

(6)YANA MAGANIN CIWON GABABUWA:

Cin Namijin goro na magance matsalar ciwon gabobi, kamar yawan gullewa da zugi, yana kuma rage kowane irin radadin azaba.

 

(7)YANA MAGANIN CUTUTTUKAN MA’AURATA (STD)

Yawan cin namijin goro na kashe kwayoyin cutar da ake dauka wajen saduwa wato STD.

 

(8)YANA MAGANIN HUNHU:

Cin namijin goro na kara lafiyar hunhun dan-Adam….

 

(9)YANA GINA GARKUWAR JIKI:

Namijin goro na da kaso mai yawa na sinadarin ‘antiodidant’ Wanda ke da muhimmancin gaske wajen yakar kwayoyin cututtuka da kuma sake gina garkuwar jikin dan-Adam.

 

(10) YANA MAGANIN ZAZZABIN CIZON SAURO:

Namijin goro rigakafi ne daga kamuwa da zazzabin cizon sauro….

 

(11)YANA KARE IDANU DAGA MAKANTA:

Cin namijin goro na kare idamu daga makancewa….

 

(12) YANA KASHE GYAMBON-CIKI

 

Mai wannan larura idan yana cin namijin goro to insha’ Allah zai warke….

Daga karshe ina son in jinjina wa wani Mai shari’a daga jihar Bauchi da ya kashe auren na biyu da wani mutu ya yi. Na san za ku ji mamaki ina murna an kashe aure amma ku biyo ni mako mai zuwa In Shaa Allah ku sha labari.

Exit mobile version