‘Yan siyasan Nijeriya sun fara muhawara kan zaben 2027, inda kowannensu ke aiki tukuru don tsare mukamansu a nan gaba. Sai dai kuma wasu gwamnonin da ke kan wa’adinsu na farko na iya yin rashin nasara a cikin zaben 2027.
Hakan zai ya faru ne saboda da yawa daga cikin gwamnonin da suka fara mulki a shekararsu ta farko sun fara ne da fadace-fadace maimakon gina kawance da habaka tsare-tsarensu na harkokin siyasa.
- Pep Guardiola Ya Tsawaita Kwantiragi A Manchester City Har Zuwa Shekarar 2027
- Shugaban Kasa: ACF Za Ta Goyi Bayan Ɗan Takarar Arewa A Zaɓen 2027
Wasu daga cikin fadace-fadacen da gwamnonin ke fafatawa suna da tasiri wajen tabbatar da sakamakon zabe a jiharsu.
Binciken da aka yi a tsanake ya nuna cewa wasu gwamnonin sun fara shekara ta farko a kan karagar mulki suna yakar ubanningidansu na siyasa ba tare da wani tsarin siyasar da zai taimaka masu wajen komawa kan mulki ba, yayin da wasu ke yakar sarakunan masu daraja ta daya, wanda a karshe suna iya harzuka jama’a su juya musa baya.
Wasu daga cikin gwamnonin da ke hasashen ba za su dawo kan mukamansu ba sun hada da Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu Sokoto, Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, Gwamnan Kaduna, Uba Sani, Gwamnan Benuwai, Hyacinth Alia, da kuma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kadan Kenan daga ciki.
Dalilan da ya sa wadannan gwamnonin da aka ambata ake hasashen ba za su koma kan mukamansu ba saboda:
Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu
Gwamnan Jihar Sakkwato na daya daga cikin gwamnonin da suke cikin wa’adi na farko a Nijeriya, wanda ake hasashen ba zai iya yin nasara a 2027 ba idan har ya yi yunkurin tsayawa takara karo na biyu. Tun kafin ya cika shekara daya a kan karagar mulki, gwamnan ya sauke wasu sarakuna kusan 15 a jihar, bisa wasu laifuka daban-daban, lamarin da ka iya janyo masa cikas a burinsa na zarcewa a kan karagar mukli karo na biyu.
Bayan ‘yan watanni ne, kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta yi korafin cewa gwamnan na shirin tsige Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar. Ko da yake gwamnatin ta musanta wannan zargi, wanda kudirin a majalisar dokokin jihar ya tsallake karatu na biyu.
Idan kudirin zama doka, za a tsige Sarkin Musulmi daga wasu mukamai da suka hada da nadin sarakuna da hakimai, ba tare da sa hannun gwamna ba. Duk da cewa ana iya daukar wannan matakin a matsayin tsarin mulki saboda dokokin da aka yi amfani da su, zai iya jawo wa gwamna asarar wa’adin mulki na biyu domin Jihar Sakkwato da kuma matsayin Sarkin Musulmi na da alaka da addini.
Jaridar Punch ta kuma ruwaito cewa wata majiyar siyasa a jihar ta bayyana cewa gwamnan da magoya bayansa ba su taba boye tunanin tsige Sarkin Musulmi daga yakin neman zabensu ba. Majiyar ta bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta yi yakin neman zabe tare da bayyana cewa, ‘sabuwar gwamnati, sabon sarki’.
Gwaman Ribas, Siminalayi Fubara
Gwamna Jihar Ribas, Fubara yana daya daga cikin gwamnoni sahu na farko da ake hasashen ba za su iya sake lashe zabe 2027, saboda rashin jituwar da ke tsakaninsa da ubangidansa na siyasa, Nyesom Wike, wanda yanzu ya zama ministan babban birnin tarayya.
Rikicin Fubara da Wike ya samo asali ne watanni uku da fara mulkinsa a matsayin gwamnan Ribas, wanda da yawa daga cikin masu lura da harkokin siyasa tsammanin haka na iya faruwa ba a cikin karamin lokaci.
Amma Shugaban kasa, Bola Tinubu ya taba yi wa Wike alkawari a bainar jama’a cewa zai kyale shi wajen kaddamar duk wani aiki a Abuja. Don haka, tare da goyon bayan tarayya da na shugaban kasa, Wike na iya kayar da Fubara ko kuma ya kulla masa makircin tsige shi kafin karshen wa’adin mulkinsa ya kare.
Haka kuma, wani manazarci Okanlawon Gaffar, a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da manema labarai, ya bayyana cewa Wike yana da kwarewa. A matsayinsa na tsohon gwamnan Jihar Ribas, ya san yadda zai yi nasara a matsayin ubangidan siyasa da kuma yadda za a iya kayar da wani a fagen harkokin siyasa.
Wani abin da bai kamata a manta da shi ba shi ne, hazakar Wike a siyasa. Ya fara siyasa ne tun a shekarar 1999. Kasancewarsa a jam’iyyar PDP da kuma yadda ya rike mukamin minista a jam’iyyar APC wata shaida ce da ke nuna hazakarsa.
Ko da yake a kwanakin baya, Gwamna Fubara ya yi nuni da cewa zai fice daga PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta gaza a wurinsa, amma a halin yanzu Wike na da karfin jam’iyyar PDP da APC a Ribas. Har yanzu dai babu tabbas ko Fubara yana da tsarin siyasa mai karfi da zai kafa jam’iyyarsa ta siyasa ko kuma ya shiga karamar jam’iyya da zai iya kayar da Wike a zabe.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kasance yana da cikin gwamnonin da ke kan wa’adinsu na farko, wanda ake ganin cewa yana da matukar wahala ya zarce zuwa wa’adi na biyu ta hanyar kuri’un jama’a idan har ba a gaggauta warware takaddamar da ke tattare da tsige Sarkin Kano ba.
Duk da cewa wanda ya gada kuma yanzu shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya sha suka a kan tsige Muhammadu Sanusi, ana zargin gwamnan da sake yin wani kuskuren da Ganduje ya yi.
A zuwa 2027, al’ummar jihar za su iya neman gwamnan da zai iya daidaita rikicin masarautun, musamman ma a yanzu da ake ganin dalilin da ya sa wasu gwamnonin suka koma tsige sarakunan gargajiya, musamman Sarkin Musulmi.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani
Gwamna Uba Sani shi ma wani gwamna ne da ke cikin wa’adinsa na farko da a halin yanzu yana fada da ubangidansa, Malam Nasir el-Rufai, ta hanyar majalisar dokokin jihar. Ba kamar Fubara ba, Sani yana da kwarewar siyasa a matsayinsa na tsohon sanata kuma ga dukkan alamu yana da goyon bayan mafi yawan ‘yan majalisar jihar.
Sai dai ga dukkan alamu tsohon gwamnan jihar na da goyon bayan al’umma, kuma hakan na iya karuwa fiye da yadda ake tsammani.
Alamu na nuni da cewa el-Rufai ma zai yi kokarin wanke sunansa, matakin farko shi ne, ya maka majalisar dokokin jihar kara a gaban kotu kan rashin sauraron karar da ‘yan majalisar suka yi masa na cin hanci da rashawa na naira biliyan 432 da ake zargin gwamnatinsa ta wawure.
Idan har el-Rufai ya samu nasara a babbar kotun Jihar Kaduna, hakan zai kara kaimi wajen hana gwamnan samun nasara a jihar a karo na biyu.
Gwamana Benuwai, Hyacinth Alia
Gwamnan Jihar Benuwai, Hyacinth Alia, shi ma ba ana hasashen zai yi wuya ya koma kan kujerarsa a 2027 idan har ya kasa samun goyon bayan sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, wanda a halin yanzu shi ne ke kuwa da tsarin jam’iyyar a jihar.
Alia ba shi da kwarewar siyasa kafin fitowarsa a matsayin dan takarar gwamna a APC a zaben 2023. Ko da yake zai yi amfani da matsayinsa wajen gina gadoji da samar da kokarin gina siyasarsa kafin 2027, dole goyon baya da karfin siyasar Akume su yi tasiri.