Wasu da ake zargi ɓata garin ne sun lalata hanyar jirgin kasa da kuma yunƙurin sace karafunan layin dogon da ke ƙauyen Chidunu a karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Mai magana da yawun hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa, Alhaji Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ƙarin haske kan koma bayan da hakan zai iya kawo wa.
- ‘Yan Ta’adda Sun Sake Sace Mutane 87 A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Kaduna
- An Gano Wasu Mutum 14 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
Abdullahi ya ce akwai buƙatar gyara layin dogon daga yanzu zuwa dare, duba da irin ƙalubalen da hakan zai iya haifarwa wajen zirga-zirgar jiragen ƙasan musamman a wannan yankin.
Abdullahi ya ce “Zai yi wahalar gaske a halin da ake ciki a iya gyara ɓarnar da aka yi daga yanzu zuwa dare”
Ya kara da cewa akwai bukatar haɗa hannu da ƴan sa-kai domin saka ido, ta yadda za a iya kare faruwar hakan a nan gaba.
Sai dai kuma jami’an tsaro sun yi nasarar kama waɗanda ake zargin da wannan aika-aikar a lokacin da suke ƙokarin guduwa da abubuwan da suka sata.
“A ranar Lahadi muka samu rahoton cewa an kama waɗanda ake zargin a manyan motoci biyu maƙare da ƙarafunan layin dogo da suka cire” Cewar Abdullahi
Abdullahi ya ce a halin yanzu Rundunar tsaro ta farin kaya ta Civil Defense reshen jihar Kaduna na gudanar da binciken lamarin.