Wasu mahara da ake zargi ‘yan ta’adda ne sun kashe mutune 14 a wani sabon hari da suka kai kusa da kauyen Chirang, da ke yankin Mangor, a Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.
Ƙungiyar Bunƙasa Al’adu ta Al’ummar Bokkos (BCDF), ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su sun faɗa tarkon maharan ne bayan yi musu ƙofar rago.
- Sojoji Sun Kwato Makamai Daga Hannun Ƴan Bindiga, Sun Ceto Yaro A Filato
- Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A Filato
Kamar yadda Shugaban ƙungiyar, Farmasum Fuddang, ya bayyana a wata sanarwa cewa yankin ya daɗe yana fuskantar hare-hare, tare da asarar rayuka da dama, ko a daren ranar Kirsimeti ma an kashe fiye da mutane 60 a wani mummunan hari shekaru biyu da suka wuce.
Sanarwar ta kara da cewa wannan sabon hari ya zo ne kwanaki biyu bayan da wani rikici ya ɓarke a yankin, wanda ya yi sanadin mutuwar wani matashi.
Ƙungiyar BCDF ta ce waɗanda harin ya rutsa da su sun haɗa da mata da ƙananan yara, a yayin da suke dawowa daga kasuwar mako-mako da ke ci a garin Bokkos.
Shugaban ƙungiyar ya ce harin ya faruwa a dai-dai lokacin da ake kokarin samar da zaman lafiya da sulhu, inda ya bayyana harin a matsayin abin Allah-waɗai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp