Maryam Laushi-Dasilba
Maryam Laushi shahararriyar a shafukan sada zaumunta mai yada labarai, mai bayar da shawara akan abin ya shafi jinsi, kuma kwararriya kan harkokin sadarwa tare da maida hankali kan sabbin kafafen yada labarai da dabarun sadarwa. A matsayinta na wanda ta kafa kungiyar Not Too Young ToRun Mobement, ta taka rawar gani wajen kokari karfafawa matasa gwiwa a harkokin siyasa, da bayar da shawarwarin daidaita jinsi, da bai wa matasa damar taka rawar gani a harkokin mulki.
Maryam ta shahara sosai wajen kokarin da take yi na inganta shigar mata a fagen siyasa da kuma kara daukaka muryar kungiyoyin da aka ware. Ita ce shugabar 00 na yau da kullun akan tattaunawar kwamiti kuma akai-akai tana hidima a matsayin mai ba da shawara, kuma mai kula da al’amuran zamantakewa da na sana’a.
Shawararta har ta wuce magana da jama’a ta kai ga rubuce-rubuce da ayyukanta na sadaukarwa, ta ci gaba da wayar da kan jama’a game da daidaiton jinsi, adalcin zamantakewa, da shigar da matasa a cikin harkokin siyasa, wanda hakan ya sa ta zama daya daga cikin masu fada a ji a fagen gwagwarmayar samar da al’umma mai hade da adalci.
Joana Nnazua Kolo
Joana Nnazua Kolo ta kasance mai ba da agajin jin kai wadda ta kafa tarihi a matsayin kwamishiniya mafi karancin shekaru a Nijeriya tana da shekaru 26.
An nada ta mukamin kwamishiniya mai Kula Da Harkokin Matasa da Wasanni a Jihar Kwara kafin makonni biyu kacal ta kammala Bautar kasar ta (NYSC) a watan Oktoban 2019, inda ta koyar a makarantar sakandare ta Model Boarding Junior da ke Garin Guri, a Jihar Jigawa.
An san Joana saboda sadaukar da kai ga ayyukan jin kai, ci gaban al’umma, da bayar da shawarwari don samar da shugabanci na gari, an nada Joana tana daya daga cikin “Manyan Mata 100 Mafi Tasiri” a Jaridar Guardian cikin 2020. Ta kuma zama mai ba da shawara kan karfafawa yara ‘yan mata shawara ga Gwamnan Jihar Kwara, tare da yin amfani da kokarinta na fafutukar kare hakkin mata matasa da samar da canji mai karfi a cikin al’ummarta.
Maryam Booth
Maryam Ado Mohammed, wacce aka fi sani da Maryam Booth, ita shahararriyar jaruma a tsangayar Kannywood wacce ta yi wani abin burgewa wanda ta yi fice saboda kwazonta a cikin The Milkmaid (2020), an ba ta babbar lambar yabo ta Africa Mobie Academy Award a matsayin mafi kyawun jarumai a cikin rawar da ta taka.
Baya ga nasarorin da ta samu a harkar fim, an nada Maryam a matsayin jakadiyar abinci ta Sumal a shekarar 2022, wanda ya kara tabbatar da tasirinta. Ita ma kwakkwaran ‘yar kasuwa ce kuma wacce ta kafa MBooth Beauty Parlour, ta jajirce wajen karfafa wasu ta hanyar kasuwancinta.
Maryam Uwais
Maryam Uwais fitacciyar lauya ce, sannan kuma ’yar kasuwa, kuma mai kokarin kare hakkin dan’Adam, ta kasance ta ba da gudunmawa sosai wajen saka hannun jari da kuma rage radadin talauci a Nijeriya. Daga shekarar 2015 zuwa 2023, ta yi aiki a matsayin mai ba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin zuba jari, inda ta taka rawar gani wajen tsarawa da aiwatar da shirin nan na ‘National Social Inbestment Programs (NSIP),’ da ke da nufin rage radadin fatara da talauci a tsakanin al’umma marasa galihu ta hanyar zamantakewa.
Ta shafe sama da shekaru 36 tana aikin shari’a, Maryam ta rike manyan mukamai a ma’aikatar masana’antu ta Jihar Kano, da Babban Bankin Nijeriya, da kuma hukumar gyara dokokin Nijeriya. Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da rahoto na musamman kan hakkin yara ga Hukumar Kare Hakkin dan Adama ta kasa kuma ta kafa shirin Isa Wali Empowerment Initiatibe a 2009 don magance matsalolin mata da farin cikin yara. Maryam ta samu da kyautuka da dama da suka hada da lambar yabo na mata masu jaruntaka na duniya da lambar yabo ta mata wadanda suka jagoranci ci gaban zamantakewar al’umma a shekarar 2022.