Dabarar koyarwa ta gane abu ta sha bambam da wadanda ake amfani da su a matsayin dabarun koyarwa amma a gargajiyance, inda gudunmawar da dalibi yake badawa ana gane ta, ta hanyar bayanain da yake samu daga wurin Malami ba tare da ya kasance ya kasance mai bayar da gudunmawa ba sosai.
Ko kuma irin gudunmawar da yake badawa bata da wani abin gamsarwa kamar yadda ya dace, wato bada amsoshin tambayoyin da Malami ya yi, ko kuma su yi wasu tambayoyi wadanda ba zai iya bada gamsassun amsoshi ba.
- Sin Ba Za Ta Canza Matsayarta Game Da Mayar Da Hankali Kan Kasashe Masu Tasowa Ba
- Gwamnatin Tarayya Da Google Sun Bullo Da Hanyar Samar Wa Da Matasa 2,500 Aikin Dogaro Da Kai
A irin wannan dabarar, babban lamari na koyarwa ya dogara ko tsaya ne akan irin kokarin da dalibai suka yi wajen bada tasu gudunmawar a cikin halin koyarwa.Koyo ta gane abinda ake koyarwa nada alaka da hanyoyi da kuma dabaru wanda mutum yake amfani da su wajen amfani da hankalin sa da ilimin da yake da shi, don bukatar daga karshe a samu cimma biyan bukata ko shi ma akan abubuwan da shi ma kan shi bai sani ba a baya.Don haka ne dabarar koyarwa ta yadda ake gano wani abu bayan koyarwar ana karuwa da hakan ne ta hanyar abubuwan da aka yi amfani da su, wajen samar da wasu sabbin dabaru ba domin komai ba saboda a samu damar cimma karuwa da bayanan da ba’a sani ba da kawo karshen lamarin (Ahmed, 2005).
Abu mai yiyuwa ne a bambance tsakanin nabyan abubuwan biyu, wanda kowane daga cikinsu ya danganta ne akan irin gudunamwar da dalibai suka bada a lokacin da ake koyarwar, kamar nau’oin haka a gaba (Ahmed, 2005):
1) Abu na farko inda dalibai suke yin aiki a karkashin Shugabancin da lurar Malami.
2) Abu na biyu yadda ake koyo da kai inda su daliban ne suke yin aikin da kansu, amma shi Malamin bai yin katsalandan sai dai idan akwai bukatar ayi gyara wuraren da aka yi kuskure, ko sun fuskanci wata matsala, ko kuma daidaita yadda ya kamata su yi tunani.
Dabarar koyarwa ta ganewa kamar ko fiye da yadda lamari yake tana da matukar amfanoni masu yawa, manya daga cikinsu sune kamar abubuwan da suke a kasa (Ahmad, 2005):
1.Hanyar kasancewar irin gudunmawar da dalibai masu koyo suke badawa a dabarar koyar da su darsi ko darussa, daibai ko ‘yan makaranta suna koyon dabarun da suke dole ne domin su gane ko sani sabbin abubuwan da za su taimaka masu a gaba.
2.Lamarin ko hakan yana taimakawa wajen inganta ilmi da tunanin inda dalibai suka sa kansu dangane hanyoyin da za suyi amfani dasu wajen maganin matsaloli, bincike.
3.Dabarar koyar da darussa ta hanyar da zata taimakawa dalibai su kara sanin hanyoyin da za su yi amfani da su wajen sanin yadda za su yi sharhi kan lamari, su yi shi, da kuma gwada su bayanai a irin tafarkin da ya dace.
4)Akwai wasu abubuwan da za’a dogara da su a matsayin sheda wato kamar samuwar ayyukan da suka shafi ilimi, mutum ya rika ji kinsa baya da wata matsalar abinda ya shige ma shi duhu idan ya kai ga ganin abin muraran.Wadannan na karka dalibai kwarin gwiwa su koyi abubuwa ba tare da matsala ba lokacin da ake koya masu darasi.
Matakan da aka amfani da su a hanyar koyo ta ganin lamarin ko gane shi sun hada da (Ahmad, 2005):
1) Mutum ko dalibi ya rika jin d alkwai matsala .
2)Mai da hankali kan wasu abubuwa da bau kamata ba su kuma da alaka da abinda ake koyo.
3) Wani abu ya faru ( gano yadda lamarin ya faru).