Wasu Shugabannin Kasashen Duniya Sun Taya JKS Murnar Cika Shekaru 100 Da Kafuwa

Daga CRI Hausa

Shugabannin jam’iyyun siyasa da gwamnatocin kasashen waje, na ci gaba da aiko sakonnin taya murnar cikar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin wato JKS shekaru 100 da kafuwa.

A cikin sakon da suka aikowa babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ko kwamitin tsakiya na JKS, sun tabo irin manyan nasarori da babbar gudummawar da JKS ta baiwa duniya a cikin shekaru 100 da suka gabata, musamman tun lokacin babban taron jam’iyyar karo 18, inda suka bayyana tabbacin cewa, JKS za ta kara cimma nasarori a nan gaba.

A nasa sakon, shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Ghazouani cewa ya yi, bayan shekaru 100 na gwagwarmaya da sadaukar da kai, JKS ta yi nasarar magance galibin manyan kalubaloli tare da jagorantar kasar Sin, zuwa kasa mai karfi a duniya.

Shi kuwa shugaban jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera cewa ya yi, al’ummar kasarsa da ta Sin, kansu a hade yake kuma ‘yan uwan juna, sun kuma himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya, da bunkasuwa da samar da farin ciki ga al’ummominsu.

Sun kuma kafa al’umma mai kyakkyawar makoma. Shugaba Touadera ya ce, yana fatan yin amfani da bikin cikar JKS shekaru 100 da kafuwa, a matsayin wata dama, ta kara inganta da zurfafa hadin gwiwar abokantaka tsakanin kasashen biyu.

Shi ma shugaban Benin Patrice Talon, a nasa sakon ya bayyana cewa, cikar JKS shekaru 100 da kafuwa, zai bude wani sabon babi na farin ciki da haske ga al’ummar Sinawa da ma bil-Adama baki daya,yana mai cewa, a shirye Benin ta ke ta zurfafa alaka da musaya a fannoni daban-daban, da kara kawo alheri ga jama’ar kasashen biyu da ma duniya baki daya.(Ibrahim)

 

Exit mobile version