Tun bayan dawowar dimokuradiyya Nijeriya a shekarar 1999, daruruwan mutane sun wakilci al’umma a mazabunsu daban-daban.
Su ‘yan majalisa ba su da ka’idar wa’adin mulki kamar yadda shugaban kasa ko gwamna ke da damar shugabanci har sau biyu ma’ana shekara 8. Hakan ya sanya wasu suke samun damar daukan shekaru masu yawan gaske a zauren majalisar tarayyar Nijeriya.
A nan ga wasu ‘yan majalisan kasa da suka kwashe sherkaru masu yawa a zauren majalisan tarayyar Nijeriya.
Nicholas Mutu
Tun da aka dawo mulkin farar hula a shekarar 1999, Hon. Nicholas Mutu ne yake wakiltar mutanen Bomadi/Patani na Jihar Delta a majalisar tarayya. Nicholas Mutu ya rike shugabancin kwamitin kula da hukumar bunkasa yankin Neja Delta tun daga 2009 har zuwa 2019.
Ahmad Lawan
A zaben 1999 ne Ahmad Ibrahim Lawan ya zama dan majalisar wakilai, mai wakiltar yankin Bade/Jakusko. A wannan kujera ne ya yi shekara takwas a karkashin jam’iyyar ANPP har zuwa 2007. A zaben na 2007 ne Ahmad Lawan ya zama Sanatan Arewacin Jihar Yobe. A 2019, ya karbi shugabancin majalisar dattawan Nijeriya har zuwa yau.
Femi Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila shi ne shugaban majalisar wakilan tarayya na kasa a yau. Dan siyasan yana kan wa’adinsa na biyar kenan a kujerar majalisa. A 2003, Femi Gbajabiamila ya zama dan majalisar yankin Surulere I, tun wancan lokaci bai fadi zabe ba. Bayan shekara 16 ya zama mutum na hudu a kasar nan.
Muhammad Ali Ndume
Shi ma Muhammad Ali Ndume ya zama dan majalisar wakilai na yankin Chibok/Damboa/Gwoza ne a 2003, ya yi shekara takwas yana rike da wannan mukami. A 2011 aka zabe shi a matsayin Sanatan Kudancin Borno, har yau kuma shi ne a kan kujerar.
Ike Ekweremadu
Ba a taba yin wanda ya dade yana jagorantar majalisar dattawa kamar Sanata Ike Ekweremadu ba. Shi ma ya zo majalisa ne a 2003, kuma ya dade ana yi da shi. Ike Ekweremadu ya shafe shekaru 12 a jere a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa. Wanda shi ne ya fi dadewa a mukami a zauren majalisa.
James Manager
Ba zai yiwu a yi maganar santaocin da suka dade ba tare da an ambaci James Manager ba. Sanatan zai cika shekara 20 yana wakiltar mutanen kudancin Delta a 2023.
Leo Ogor
Wani dan siyasa da ya tare a majalisar tarayya Nijeriya tun 2003 shi ne Leo Ogor. A shekara mai zuwa dan majalisar na Isoko-North/Isoko-South zai cika shekara 20.
Alhassan Ado-Doguwa
Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado-Doguwa ya zo majalisa ne a 2007. Ana tunanin yana harin shugaban majalisa idan ya zarce a 2023. Shi ne dan majalisa na farko a tarihin Nijeriya wanda yana kammala bautar kasarsa aka rantsar da shi majalisa.
Mohammed Monguno
Wani wanda ya dade a majalisa kuma yana neman shugabanci shi ne Hon. Mohammed Monguno mai wakiltar Marte/Monguno/Nganzai, sau biyar ana rantsar da shi.
Kabiru Ibrahim Gaya
A shekarar 2007 ne Kabiru Ibrahim Gaya ya zama Sanatan Kudancin Kano a majalisar dattawa. Tsohon gwamnan Jihar Kano ne a jamhoriya ta uku karkashin rusasshiyar jam’iyyar NRC. A zabe mai zuwa shi ne zai sake tsaya wa jam’iyyar APC takara a Kano.
Enyinnaya Abaribe
Bayan rikicinsa da Gwamnansa a 2007, Enyinnaya Abaribe ya zama Sanatan Abiya ta Kudu a majalisa, shekararsa 15 kenan bai motsa daga majalisar dattawan ba. A 1999 shi ne mataimakin gwamnan Jihar Abiya.
Yakubu Dogara
Tsohon shugaban majaliar wakilai Yakubu Dogara yana cikin wadanda suka ga jiya da yau a majalisa, tun 2007 yake wakiltar Bogoro, Dass da Tafawa Balewa. Ya yi shugaban masu rinjaye da shugaban marasa rinjaye a zauren majalisar.
Mukhtar Betara
Wani dan majalisan Borno da ya dade a zauren majalisa shi ne mai wakiltar mazabun Biu/Bayo/Shani, a 2007 Mukhtar Betara ya zo majalisa, kuma babu mamaki ya zarce har 2023. Yana daya daga cikin wadanda ake hasashen za su shugabanci majalisar idan ya zarce.
Khadijah Abba-Ibrahim
Babu macen da ta dade a majalisa kamar Khadijah Abba-Ibrahim mai wakiltar Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa, sau biyar tana cin zabe a yankinta na Jihar Yobe. A shekarar 2016, Shugaba Buhari ya nada ta ministar harkokin waje, amma a watan Janairu ta ajiye mukamin ta sake tsayawa takara ta kuma sami nasara. Ta ma taba yin takara da dan kishiyarta.
Wai shin wadannan mutane da suka dade a majalisa haka sun fi kowa cancanta ne a mazabunsu?