An gano gawawwakin wasu yara biyar a cikin wata mota da aka yasar a Minna da ke Jihar Neja, a yammacin ranar Lahadin da ta gabata.
Wannan bala’i, ya afku ne a garin Minna ta Jihar Neja; a yammacin ranar Lahadi, yayin da wasu yara su biyar suka kulle kansu a cikin wata mota na tsawon sa’o’i biyar; bisa kuskure, dukkanninsu kuma suka mutu sakamakon rashin samun damar yin numfashi.
- An Haramta Hawan Doki Yayin Bukukuwan Sallah A Neja
- Yadda Za Mu Fahimci Kuskuren Amurka Na Cewa Wai Kasar Sin “Ta Wuce Gona Da Iri” Wajen Samar Da Hajoji
Wannan iftila’i da ya faru a garin Gurara Albishir da ke kan titin Bidda na garin Minna, ya yi matukar jefa al’ummar wannan gari cikin alhini.
Binciken Jaridar LEADERSHIP ya gano cewa, yaran suna yin wasa ne a wani katafaren gida da ke kusa da gidansu, inda suka kulle kansu bisa kuskure a cikin wata mota kirar Honda da aka jima da yin watsi da ita har tsawon shekaru biyu.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, tun misalin karfe 11:00 na safe ne; wadannan yara suka kulle kansu, yayin da kuma iyayensu ke can suna ta faman neman su; ba su gan su ba, har sai lokacin da aka gano gawarwakinsu a cikin wannan mota da misalin karfe 4:00 na yamma.
Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa; wadanda wannan iftila’i ya rutsa da su, hudu mata ne da kuma namiji daya; sannan uku daga cikinsu ‘yan’uwan juna ne, wadanda su kenan iyayensu suka haifa a duniya. Sauran biyun kuma da suka mutu, iyayensu daban-daban ne; ciki har da shi kansa mai motar.
Haka zalika, an bayyana sunan wadannan yara da shekarunsu kamar haka: Zahra ‘yar shekara 10, Aisha mai shekaru 7, Fati ‘yar shekara 5 da kuma Isah dan shekara 7, duk dai da cewa LEADERSHIP ta kasa tantance ko wane ne cikon na 5 din.
Shugaban Karamar Hukumar Chanchaga, Aminu Ladan; wanda gidansa ke kusa da unguwar da wannan al’amari ya faru, ya ziyarci wajen ba tare da wani bata lokaci ba.
Kazalika, ya tabbatar wa da manema labarai faruwar wannan al’amari tare da bayyana iftila’in a matsayin wani babban abin takaici, sannan kuma a karshe ya jajanta wa iyayen wadannan yara da suka rasu.
Bugu da kari, har zuwa lokacin hada wannan rahoto; ba mu samu damar jin ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yansanda (PPRO), Wasiu Abiodun ba.