Wata ƙungiya mai zaman kanta, Patriots for the Advancement of Peace and Social Development, ta shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja tana zargin Ofishin Sakataran Gwamnatin Tarayya (OSGF) da ƙin miƙa takardun karatun ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.
Ƙarar da aka shigar, mai lamba FHC/ABM/CS/2449/2025 kuma aka rubuta ranar 14 ga Nuwamba, na neman kotu ta bayar da umarnin tilasta OSGF ta miƙa kundin bayanai (CV) na ministan da sauran takardun da ya gabatar lokacin zaɓensa a muƙamin.
- Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle
- Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya
Bisa bayanan da aka kai kotu, ƙungiyar ta nemi bayanan ne bisa dokar Freedom of Information Act (FOI), amma OSGF ta ƙi bayarwa suna dogaro da sashi na 14(1) da ke kare bayanan sirri. Lauyan ƙungiyar, Mubarak Bala, ya buƙaci kotun ta tantance ko hakan ya yi daidai da dokar, ganin cewa dashi na 1, 2(6), 4 da 7 na FOI suna ba da dama a samu irin waɗannan bayanai, musamman idan akwai zai kawo maslaha ga jama’a.
Ƙungiyar na neman kotu ta ayyana cewa ƙin bayar da bayanan ya saɓa doka, tare da bayyana cewa takardun da minista ya gabatar don samun muƙamin takardu ne na gwamnati kuma jama’a na da haƙƙin bibiyarsu.
Haka kuma, suna neman kotu ta tilasta a miƙa CV ko kuma cikakken takaitaccen bayani game da shi, tare da umartar waɗanda ake ƙara.
Har yanzu ba a saka ranar sauraron ƙarar ba.













