Wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Women Centre for Self Empowerment and Development (WOCSED)’ ta bukaci zawarawa da matan da mazajensu suka mutu da su rungumi sana’o’in dogaro da kai don tallafa wa rayuwarsu da na iyalansu.
Shugabar kungiyar, Misis Onyeka Obi, ta bayar da wannan shawarar a yayin da kungiyar ke bikin ranar matan da mazajensu suka mu ta majalsar dinkin duniya a garin Inugu.
- Matasa Za Su Yi Rayuwa Mai Kyau Idan Na Zama Shugaban Kasa —Kwankwaso
- Kalubalen Tsaro: Gwamnatin Zamfara Na Shirin Kafa Sabuwar Hukumar Tsaro Ta (CPG)
Ta ce, rungumar sana’a zai taikama wa rayuwarsu zai kuma tsirar da su daga kangin talauci, wanda miliyoyin mata da mazajen su suka mutu ke fuskanta a sassan duniya.
Ta kuma kara da cewa, rashin miji na jefa mata cikin matsaloli da dama da suka hada da tsananin damuwa, talauci da cututtuka irinsu kanjamau.
Ta ce, “Suna fuskantar matsaloli da dama kuma ba a sanin irin halin da suke ciki kuma gashi al’umma basu damuwa da halin da suke ciki ba ballantana su taimaka musu.
A ranar 23 ga watan Yuni ne ake bikin ranar matan da mazajen su mutu na duniya, don jawo hankalin al’umma a kan irin halin da matan ke ciki da kuma yekuwar kai musu dauki.