Daya daga cikin marubuta littattafan Hausa na yanar gizo, YAREEMA SHAHEED ya bayyana wa masu karatu wasu batutuwa da suka faru da shi sanadiyyar rubutu, tare da bayyana irin gwagwarmayar da ya sha kafin ya fara rubutu.
Ga dai tattaunawa tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU kamar haka:
Ya sunan malamin?
Sunana Yareema Shaheed (Abou Hashmat).
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
An haife ni a garin Kaduna, na yi karatun firamare da sakandare duk a garin Jos, na je Katsina na yi karatun kiwon lafiya.
Me ya ja hankalinka har ka fara rubutu?
Abin da ya sa na tsunduma rubutu dan in fadakar tare da ilmantarwa.
Kamar wanne bangare kafi mayar da hankali a kai wajen yin rubutu?
Na fi mayar da hankalina kan zamantakewa da sarauta da dai sauransu.
Ya gwagwarmayar fara rubutun ya kasance?
Na sha wuya lokacin da na fara rubutu, domin na bibiyi manyan marubuta su saka ni a hanya wasu suka dinga yawo da hankalina, hakan ya sa na tsunduma rubutu da kaina a karshe makaranta suka karbe ni hannu bibbiyu.
Lokacin da iyayenka suka fara sani, shin ka samu wani kalubale daga gare su?
Eh! To, gaskiya na dan samu matsala kadan, saboda ni na fito daga gidan sarauta.
Daga lokacin da ka fara rubutu zuwa yanzu ka rubuta labari ya kai kamar guda nawa?
Na rubuta littattafai da yawa daga ciki akwai; Umarnin uba, Aure nake so, Saurayina Ne Sila, Hawayen Jini, Shaheed da Shaheedah, My Destiny, Maisara da sai sauransu.
Ka taba buga labarinka cikin labarun daka rubuta?
Na taba buga ‘Mu bi iyaye’.
Wanne labari ne ya zamo bakandamiyarka cikin wanda ka rubuta?
Hawayen Jini, Shaheed da Shaheedah.
Wanne irin nasarori ka samu game da rubutu?
Nasarorin dana samu ba zan iya lissafawa ba, rubutu ya kaini inda ban taba zatan zan je ba.
Wanne irin kalubale ka taba fuskanta game da rubutu?
Akwai wata mata ta taba kirana cikin dare tana zagina akan littafin UMARNIN UBA, wai na ci zarafin tauraruwar labarin, har da kukanta sosai.
Ya ka dauki rubutu a wajenka?
Na dauki rubutu a matsayin sana’a da kuma hanyar da zan isar da sako cikin sauki.
Mene ne burinka na gaba game da rubutu?
Burina na kara suna a duniyar rubutu, na kai inda ban zata ba.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ka taba iya mantawa da shi ba?
Ina tuna ranar da ina tafiya zuwa Abuja a cikin mota na ji fasinjas mata suna fira akan littattafana, ba su san ni ne ba, har tana cewa; “YAREEMA SHAHEED ai yana ban mamaki wajen rubutu sai ka ga kamar an zo karshe sai kuma ka ga an ci gaba, ke ni fa na dauka mace ce marubuciyar, ashe namiji ne. Ina mamakin yadda yake fitar da komai a gurin daya da ce, na gaishe da gwarzo”.
Bayan rubutu kana sana’a?
Ni likita ne.
Ya ka ke iya hada rubutunka da kuma aikinka?
Kowanne na ware masa lokacinsa.
Kamar da wanne lokaci ka fi jin dadin yin rubutu?
Da yamma ko lokacin da nake tafiya ko nake cin abinci.
Me za ka ce da masu karanta labaranka?
Ina kira ga makaranta labarina cewa; nan da ranar Juma’a zan fara sakin sabbin littattafaina guda biyu; Katangar Sikari, Matan Fada.
Ko kanada wadanda za ka gaisar?
Ina gaida Maimartaba Sarkin Kano da Matata Uwar ‘Ya’yana Ummu Hashmat, ina gaida Zainab Sulaiman Zeety, ina gaida Gimbiya Rahma, ina gaida Muhammad Adam Sameeru.
Muna godiya