Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, tayin muƙamin jakada a ɗaya daga ƙasashen Afrika, kamar yadda wata majiya mai tushe ta tabbatar.
Kazalika, majiyar ta ce shugaban ya wakilta shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya sanar da Ganduje.
- Shekaru 60: DICON Ta Taimaka Wajen Samar Mana Da Makamai – Janar Musa
- Shugaban Majalisa Ya Janye Ƙudirin Dokar Dauri Ga Wanda Ya Ki Rera Taken Nijeriya
An naɗa Ganduje, a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a ranar 3 ga watan Agusta 2023, biyo bayan murabus ɗin da Abdullahi Adamu.
A cewar majiyar Akpabio, ya shaida wa Ganduje tayin shugaban ƙasar na da nufin ceto shi daga shari’ar cin hanci da rashawa da yake fuskanta a Kano game da faifan bidiyon Dala na shekarar 2018.
Ya ce bidiyon ya janyo masa ba’a da gori a bainar jama’a, tare da matarsa da ɗansa da kuma sauran masu hannu cikin lamarin na sama da Naira biliyan 50.
Sai dai wata majiya, ta ce Ganduje ya ƙi amincewa da tayin, inda ya bayyana cewa zargin ƙarya ne, kuma zai yi nasara a shari’arsa a kotu wanda shugaban Tinubu da kansa ya sanar da Ganduje shiri na diflomasiyya tare da ba shi damar zaɓar wata ƙasa a Afirka.
Wata majiya ta kusa da Ganduje ta ce abin da shugaba Tinubu, ya fi so shi ne ya naɗa shi Jakadan Nijeriya a ƙasar Chadi, duba da cewar ya taɓa yin aiki a Ndjamena a matsayin babban sakataren hukumar kula da tafkin Chadi tsakanin 2009 zuwa 2011.
Jaridar Daily Nigeria ta ruwaito cewa kwanaki kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya sanar da matakin ga Ganduje, an aike masa da wasiƙar wa’adi game da buƙatar ya gudanar da babban taron majalisar jam’iyyar APC na ƙasa.
Wasikar mai ɗauke da kwanan wata 9 ga watan Agusta, da sa hannun Shugaban Hadiman Tinubu, Femi Gbajabiamila, ta sanar da Ganduje cewa shugaban ƙasa zai samu halartar taron Majalisar Jam’iyyar a ranar 8 zuwa 19 ga Satumba, 2024.
Ko da aka tuntuɓi mai magana da yawun Ganduje, Edwin Olofu, ya ce mai gidansa bai yi masa bayani kan batun ba amma ya tabbatar da amincewar shugaban ƙasa na a gudanar da babban taron jam’iyyar.