Wata Sabuwa: Masu Mata Sama Da Daya Sun Fi Dadewa A Duniya?

Binciken da masana kimiyya suka yi a kasashe 140 na duniya ya nuna yadda auren mace sama da daya ke taimakawa wajen yin rayuwa mai tsawo.

Wannan bincike dai kamar yadda kafar yanar gizon ‘trt.net.tr’ ya bayyana, ya nuna sabanin yadda wasu suke nuna cewa, auran mace sama da daya na sam aza mutuwa da wuri.

Binciken da aka yi ya tabbatar da cewa, mazan da suka fito daga al’ummu da suke auran mace sama da daya sun fi wadanda suka fito daga inda ake auren mace daya kawai.

Wata malamar sanin rayuwar dan adam a jami’ar Sheffield da ke Birtaniya mai suna Birpi Lummaa ta ce, sakamakon binciken da suka yi a kasashe 140 ya nuna musu yadda mutane 60 daga kasashe masu auren mace sama da daya suke samun karin shekaru 12 na rayuwa sama da wadanda suka fito daga kasashen da ba a auran mace sama da daya.

Lummaa ta gabatar da binciken nata a makon da ya gabata a yayin taron shekara-shekara na kungiyar malaman sanin rayuwar dan adam da halitta da aka gudanar a birnin New York na Amurka.

Babban sirrin rayuwa mai tsayi shi ne auran mace sama da daya. Sakamakon binciken ya kuma nuna yadda alkaluman Hukumar kula da Lafiya ta Duniya suka nuna masu auren sama da mace daya sun fi samun cikakkiyar lafiya.

Masaniyar kimiyya mai suna Lance Workman ma ta ce, bincikensu ya nuna musu tabbacin cewa, masu mata sama da daya sun fi samun lafiyar jiki da rayuwa mai tsawo sama da wadanda ba sa yin aure ko suke zama da mace daya kawai.

Mene ne ra’ayinku? Shin da gaske ne? Ko kuna da wani ra’ayi na daban? Sai na ji daga gare ku.

 

Na ku, Abban Umma (B/014/Z/KAD). 08033225331

*Mun dauko wannan ne daga yanar gizon ‘TRT HAUSA.COM’

Exit mobile version