Abba Ibrahim Wada" />

Watakila Carrick Ya Zama Mataimakin Mourinho

 

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana cewa baya tunanin zai nemi wanda zai zama mataimakinsa a kungiyar bayan da mataimakinsa da suka dade suna aiki tare zai bar kungiyar a karshen wannan kakar.

Mourinho ya bayyana hakane a wata hira da yayi da manema labarai bayan da kungiyarsa ta buga wasanta na karshe a gasar firimiyar wannan shekarar a gida da kunfiyar Watford wasan da aka tashi 1-0 kuma Marcus Rashford ne ya zura kwallon.

Ya ci gaba da cewa zaiyi kokari yaga ya tsara wadanda zasu cigaba da taimaka masa amma batare daya fitar da takamemen wanda zaiyi aiki a matsayin mataimakinsa ba saboda ya yarda da ragowar masu taimaka masa kuma zaiyi aiki tare dasu.

Mataimakin Mourinho, Rui Faria dai ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar ta Manchester United domin shima yaje yafara aiki a matsayin cikakken mai koyarwa ba mataimaki ba bayan daya shafe shekaru 17 yana aiki tare da Mourinho a matsayin mataimaki.

Sai dai Mourinho ya bayyana cewa zaiyi amfani da tsohon dan wasan kungiyar, Machael Carrick, wanda yayi ritaya a karshen wannan kakar a matsayin daya daga cikin masu taimaka masa wajen gudanar da aiki a kungiyar.

Ya kara da cewa Carrick zaiyi aiki dashi kuma zai samu cikakkiyar dama idan ya kammala karatunsa da yakeyi a yanzu na  samun cikakkiyar shaidar koyarwa.

Manchester United dai zata fafata wasan karshe na cin kofin kalubale na FA da kungiyar Chelsea a ranar Asabar mai zuwa a filin wasa na Wembley dake birnin Landan.

Exit mobile version