Abba Ibrahim Wada" />

Watakila Samuel Umtiti Yakoma Manchester United

Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa watakila dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Samuel Umtiti yakoma Manchester United a kakar wasa mai zuwa bayan da yanzu baya samun buga wasa a kungiyar.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai tad ade tana zawarcin dan wasan baya kuma a kwanakin baya said a aka danganta Umtiti da komawa Manchester United kafin yafara jin ciwo akai-akai.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai tana fatan siyan dan wasan baya na Ajad, Matthijs De Light dan kasar Holland bayan da a kwanakin baya Barcelona ta siyi abokin wasan san a Ajad Cin wato De Jong.
Umtiti dai ya bugawa Barcelona wasanni da dama a kakar wasan data gabata tun bayan komawarsa kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Lyon ta kasar Faransa kuma ya wakilci kasar Farans a gasar cin kofin duniya.
Sai dai a wannan kakar wasanni 10 kacal ya buga da kungiyar wanda wannan shine dalilin dayasa kungiyar ta Barcelona take ganin zata iya siyar da dan wasan domin siyan wani dan wasan na baya.
Manchester United da tana zawarcin ‘yan wasan baya kuma shima Umtiti, mai shekara 25 a duniya yana daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar zata tuntuba sai dai ana ganin kudinsa zai kai fam miliyan 60.

Exit mobile version