Wasu rahotanni daga kasar Italiya sun ruwaito cewa watakila tsohon dan wasan tawagar kasar Faransa, Zinadine Zidane, ya koma koyar da kungiyar Juventus da koyarwa, idan har ya bar kungiyar Real Madrid a karshen kakar wasa ta bana.
A kwanakin baya ne Zinedine Zidane, wanda ya taba bugawa Juventus wasa a shekarun baya ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin yin hannun riga da Real Madrid a karshen wannan kaka da muke ciki duba da yadda yake ganin yanayin al’amura a kungiyar babu tabbas.
Rahotanni dai na cewa Zidane ya bukaci hukumomin kungiyar su sayo mai ‘yan wasa da suka hada da Paul Pogba na Manchester United da Sadio Mane na Liberpool da Eduardo Camabinga, amma maimakon haka suka bar shi da ‘yan wasan da ba sa iya rawar gaban hantsi.
Mujallar Dariogol da ake wallafawa a kasar Spain ta ruwaito cewa Zidane zai yi hannun riga da Bernabeu a karshen wannan kaka a matsayin sakamakon tattaunawar fahimtar juna da suka yi da shugaban gudanarwar kungiyar.
Sai dai wasu rahotanni kuma sun bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar Florentino Perez ya yiwa Zidane alwashin cewa a karshen kakar wasa kungiyar zata saki kudade domin sayan ‘yan wasan da zasu karawa kungiyar karfi.
Sai dai babu tabbas idan kungiyar zata iya sayan ‘yan wasan da Zidane yake fatan yin aiki dasu duba da irin halin matsin tattalin arzikin da duniya ta shiga sakamakon annobar cutar Korona wadda ta talauta kungiyoyi kuma hakan yasa ake ganin zai iya komawa tsohuwar kungiyar daya bugawa kwallo a baya domin ya koyar da ita.
Kawo yanzu dai Andre Pirlo shi ne yake koyar da kungiyar Juventus amma duk da haka kungiyar bata buga wasa kamar na kakar data gabata kuma kungiyar tana mataki na uku akan teburin Siriya A bugu da kari canjaras shida kungiyar ta buga a wannan kakar.
A kakar wasa mai zuwa Juventus zata fitar da kudi domin sayan manyan ‘yan wasa ciki har da Paul Pogba da Kylian Mbappe wanda hakan yasa ake ganin Zidane zai koma Juventus din da koyarwa
Yau Za A Cigaba Da Buga Wasannin Laliga
A yau Talata za a ci gaba da buga wasannin...