Shugaban hukumar zabe a jihar Katsina Alhaji Jibrin Ibrahim Zarewa, ya ba da tabbacin hada karfe da karfe da kungiyar darika awareness forum, wajan ci gaba da wayar da kan jama’a a kan abin da ya shafi hukumar zabe da kuma rijistar katin zabe da ake gudanarwa a fadin Nijeriya.
Zarewa ya bayyana haka a lokacin da shuwagabannin kungiyar suka kai masa ziyara a shalkwatar hukumar da ke Katsina.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Kansila A Adamawa
- ‘Yan Sanda Da ‘Yan Kasuwa Sun Yi Hadin Guiwa Don Kawo Karshen Kwacen Waya A Kano
Tunda farko dai shugaban ya yi wa tawagar kungiyar cikakken bayani game da ita kanta hukumar zabe da kuma irin ayyukan da doka ta sahale mata ta yi akan fannoni daban-daban.
Ya kuma nuna jin dadinsa da ziyarar tare da fadin cewa INEC a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da kungiyar, musamman a kan abinbda ya shafi wayar da kan jama’a kan batun katin zabe da sauran batutuwa a fadin jihar Katsina.
Haka kuma Zarewa, ya ce wannan ziyara an yi ta a lokacin da ya da ce, duk da cewa wuri ya kure amma dai kungiyar na da rawar da zata taka wajen ganin an kara samun narasa.
“Wani abu da ba ku sani ba shi ne, an yi wa jihar Katsina nisa wajen yin rijistar katin zabe, idan aka duba matsayin jihar Katsina ta hudu a yawan mutane da masu katin zaɓe, amma yanzu ta koma ta ashirin da hudu, wanda ba haka muka so ba” inji shi
Kazalika ya yi dogon bayani a kan yadda suka samu karin rumfunan zabe da wuraren da aka kai su, tare da daukar alkawarin cewa duk lokacin da hukumar za ta yi wani taro na masu ruwa da tsaki kungiyar na cikin sahun gaba saboda muhimmanci da irin tsare-tsaren da suke da shi.
Tunda da farko da yake nasa jawabin a kan makasudin wannan ziyara ta su, shugaban tafiyar kuma daya daga cikin kwamitin amintattu na kungiyar, Farfesa Abdulaziz Ahmad Mashi, ya bayyana cewa tuni suka so kawo ziyara amma yanzu Allah baya kaddara hakan.
Ya kara da cewa suna son hada gwuiwa da hukumar zabe domin ba da ta su gudunmawar wajen ganin jama’a sun yanki katin zabe kuma kungiyarsu ba ta da alaka ta nesa ko ta kusa da kowace irin jam’iyyar siyasa.
Farfesa Mashi, ya ce bisa haka ne suke neman cikakken bayani game da ayyukan wannan hukuma wanda hakan zai ba su damar sanin ta inda za su ba da gudunmawa ganin cewa mafi yawansu a tafiyar matasa ne.
Sannan ya nemi hukumar zabe da ta dauki kungiyar a matsayin abokiyar tafiya wajen isar da sako ga al’ummar Musulmi ba wai sai ‘yan darika kawai ba.
A nasa ta’alikin sakataren tsare -tsaren kungiyar, Awwal Abba Yahaya, ya ba da tarihin kafuwar kungiyar da kuma dalilin da ya sa aka kafa ta tare da yin bayanin irin tsarin shugabancin da suke da shi a matakin jiha da shiyya da kananan hukumomi zuwa mazabu.
Abba ya ce suna amfani da hanya mafi sauki wajen isar da kowane irin sako ake son isarwa ga mambobinsu, ko dai ta hanyar haduwa a Masallatai na yau da kullum ko kuma duk sati wajen zikirin Juma’a.
“Kimanin shekaru bakwai ke nan da kafa wannan kungiya wanda take da wakilin kowane bangare a darika kuma muna da shugabanni tun daga matakin jiha da shiyya da kuma kananan hukumomi, har da matakin rumfa, kuma babu ruwanmu da wata jam’iyyar siyasa, muna yin wanna tafiya ne ganin yadda aka bar mu a baya akan batun siyasa amma yanzu mun farka kuma za a damu da mu” inji shi
Daga karshe sakataran tsare-tsaren, ya ce sun shirya tsaf domin ci gaba da wayar da jama’a a kan wannan hidima ta katin zabe, inda ya ce za su yi amfani da kafafen yada labarai wajen isar da sakon, tare da ba da tabbacin za a ga canji nan kusa ba nesa ba.