A wannan zamani da muke ciki, amfani da fasahar sadarwa da yanar gizo ya zama jigo a rayuwar yau da kullum. Amma tare da wannan ci gaba, akwai barazana da dama da ke tattare da amfani da intanet, musamman ga wadanda ba su da cikakken ilimi ko wayewa game da yadda za su kare kansu a duniyar cyber.
Mece Ce Wayar Da Kai Kan Cyber?
- Kwararru Sun Yi Musayar Ra’ayoyi Dangane Da Wayewar Kan Sin Da Afirka
- Yadda Hukuncin Kotun Koli Ya Kara Dagula Rikicin Shugabanci A PDP Da LP
Wayar da kai kan cyber na nufin ilimantar da mutane game da yadda suke amfani da na’urori, yanar gizo, da manhajoji ta hanyar da ba za ta cutar da su ba. Ana koya musu yadda za su kare bayanansu, su gane damfara, su guji shiga shafuka masu hatsari, da kuma yadda za su kare kansu daga hare-haren yanar gizo (cyber-attacks).
Muhimmancin Wayar Da Kai Kan Cyber
· Kariya daga barazanar yanar gizo: Wadanda suka samu ilimi kan tsaron cyber sun fi iya kare kansu daga masu satar bayanai da masu fashi da makami ta yanar gizo.
· Amfani da intanet cikin tsaro: Wayar da kai tana koya maka yadda za ka yi amfani da wayar salula, kwamfuta, da sauran na’urori cikin kwarewa da tsaro.
· Sanin sirrinka da darajarsa: Mutum zai fi kulawa da bayanansa na sirri da yadda za su iya amfani da su wajen cutar da shi idan ya samu ilimi.
Abubuwan Da Ya Kamata Ka Kula Da Su
1. Kada ka bude kowanne sako ko imel da bai fito daga tushe da ka yarda da shi ba.
2. Kar ka rika danna kowanne link da ba ka tabbatar da amincinsa ba.
3. Rika sabunta (update) wayarka ko kwamfutarka domin gyara kura-kurai na tsaro.
4. Amfani da kalmar sirri (password) mai karfi da bambanta lambobi da haruffa.
5. Kada ka bayyana bayanan banki, katin ATM, ko lambarka ta sirri a dandalin sada zumunta.
Kammalawa
Wayar da kai kan cyber ba wai na ‘yan kasuwa da ma’aikata bane kadai ba. Kowa na bukatar hakan – dalibi, mai sayar da kaya, iyaye da yara. Mu dauki mataki tun yanzu domin kare kanmu da iyalanmu daga barazanar cyber.
Ku ci gaba da kasancewa da mu domin koyon dabarun tsare kai a intanet. Cyber Awareness shine matakin farko zuwa Cyber Security!
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp