Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya soke takardar filayen da aka bai wasu manyan ƴan Nijeriya, ciki har da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) George Akume.
Wannan mataki, wanda ya shafi mutane 759 da ƙungiyoyin a yankin Maitama II Abuja, an bayyana shi cikin sanarwa ne daga hukumar babban birnin tarayya. Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne sakamakon rashin biyan kuɗin takardun shaida na mallakar ƙasa (C-of-O).
- Gwarzon Shekarar 2024: Barr. Nyesom Ezenwo Wike
- Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Sunan Jami’ar Abuja Zuwa Jami’ar Yakubu Gowon
A cikin wata sanarwa daban, ministan ya ba da gargadi mai ƙarfi ga wasu masu filaye, ciki har da shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Kingsley Chinda, tsofaffin shugaban majalisar dattijai Iyorchia Ayu da Ameh Ebute, da Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Tahir Monguno, da sauran mutane 610.
An ba su wa’adin makonni biyu don biyan kuɗin da ake bin su ba shi ko kuma za su fuskanci matakin soke filin nasu kamar yadda aka yi wa wasu.