Gidauniyar ‘Wunti Al-Khair Foundation’ ta horar da ‘yan agajin kungiyoyin Addini Musulunci don sanin dabarun yadda za su shawo kan cunkoso da saukaka zirga-zirga a lokacin bukukuwan karamar sallah a Jihar Bauchi.
Wani dan Jihar Bauchi da ya kasance mai gudanar da ayyukan taimakon al’umma da na jiin kai, Alhaji Bala Wunti, ne shugaban gidauniyar kuma shi ke daukan nauyin horo na tsawon kwanaki biyu da ya gudana a babban masallacin Fadar Sarki da ke Bauchi.
- Al’adar Kallon Furannin Magnolia A Wurin Ibada Na Dajuesi Mai Tarihin Fiye Da Shekara Dubu
- Sai A Hankali Zan Gyara Chelsea, Frank Lampard
Da ya ke jawabin bude horo, daraktan sashin agaji na Jama’atu Nasril Islam (JNI) Alhaji Bala Ibrahim Sani, ya ce, horon wanda Bala Wunti ya saba daukan nauyi na taimakawa sosai wa ‘yan agajin ta hanyar basu karin ilimin da ke taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
Sani wanda shi ne Lifidin Bauchi ya ce, wannan horon shi ne karo na biyar da gidauniyar ke yi, ya misalta hakan a matsayin aikin aikairi sosai, “Iyaka abun da za mu ce wa Bala Wunti sai dai mu masa Allah ya saka masa da mafificiyar alkairi bisa irin gudunmawar da yake bayar wa addinin musulunci.”
Ya ce, a kalla ‘yan agaji 150 ne aka basu horon da za su je su ma su koyar da sauran abokan aikinsu ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Ya kara da cewa an dauko jami’ai daga hukumar kiyaye aukuwar hadura (FRSC) da Red Cross da sauran hukumomin da abun ya shafa inda suke bai wa ‘yan agajin lakcoci da darussan da suka dace dukka domin tabbatar da an yi bikin sallah lafiya.
“Kuma muna da jami’an da suke yawan zuwa aikin hajji su na nazartar yadda ake shawo kan cinkoso da tabbatar da an kammala komai lafiya, don haka irin wannan horon na kara mana saninmu da gogewa a bangaren ayyukan hidimta wa jama’a da muke yi.”
A cewarsa a karshen bitan, gidauniyar na raba kyautar buhun shinkafa, shadda da zani ga kowani mahalaccin bitar.
Kwamandan ya yi amfani da wannan damar wajen rokon Bala Wunti da ya duba yiyuwar samar wa kungiyoyin agaji da motocin daukan marasa lafiya a cibiyoyin addinin musulunci da Masallatai.
Ya ce, “Duk shekara idan wasu ‘yan agaji sun zo a wata shekara sai a canza a kawo wasu, hikimar haka shi ne kowa zai samu ilimin da ake nema.”
A cewarsa kowace shekara ana horar da ‘yan agajin ne kan yadda za su kiyaye cinkoson ababen hawa tare da saukaka wa jama’a yadda za su yi zirga-zirga a lokacin bukukuwan sallah. Sai ya ce a bana sun kara gayyato jami’ai daga hukumar kashe gobara domin basu horon kan kashe gobara musamman a lokacin da ake bukatar agajin gaggawa.
A nasa jawabin wani malamin addinin musulunci a jihar Bauchi, Sheikh Bala Isa ya nuna matukar farin cikinsa a bisa yadda Bala Wunti ke gudanar da ayyukan taimakon al’umma da suka kunshi Gina masallatai, cibiyar da mabukata, tallafa wa marasa karfi da dai sauransu.
Ya ce, horon ya zama wani karin hadin kai a tsakanin kungiyoyin agaji, ya ce taimakon da wannan horon bayarwa ba karamin fa’ida yake da shi ba. Ya bayyana cewar wannan horaswar zai taimaka gaya domin kuwa ‘yan agajin su na buqatar karin sani kan hidimar inganta aikinsu domin samun dabararrun aiki.
A nasa jawabin, Alhaji Bala Wunti, ya ce, yana shirya horaswar ne da nufin taimakawa wajen ganin an gudanar da sallar Idi lafiya ba tare da wani matsala ba.
Bala Wunti wanda shi ne babban manajan rukunin ‘National Petroleum Investment Management Services’ (NAPIMS), wanda ya samu wakilcin Kabiru Garba Aminu, ya nuna kwarin guiwarsa na cewa da irin wannan hadin kan da ake samu tsakanin kungiyoyin agaji za a kara samun kyakkyawar fahimta. Ya nemi masu samun horon da su maida hankali su ribanci abun da ake koya musu.
Alhaji Bala Wunti ya shaida cewar manufar shirya taron sh ine domin a samar wa ‘yan agajin ilimin sanin makamar aiki kamar yadda ya dace, yana mai shaida cewar mafiya yawan qungiyoyin agaji na addini basu da cikakken ilimin yadda za su bayar da agajin gaggawa ko kuma magance wani matsalar masu kawo cikas a lokacin da suke bakin aikinsu, sai ya bayyana cewar hakan ne ya sanya shirya taron domin a samar da ci gaba.