Shekaru da dama da suka wuce, wuraren da ake samun mace-macen mutane masu yawa a Nijeriya sune ta hanyar hadurran mota, farmakin ‘yan fashi da makami da kuma rikice-rikicien da suke tasow a tsakanin al’umma, amma kuma a shekaru kamar goma da suka wuce an samu wasu hanyoyin mace-macen da suka hada da ayyukan ta’addanci da na ‘yan ta’adda, garkuwa da mutane da kuma rikice-rikicen makiyaya da manoma, wasu hanyoyin sun kuma hada da na ‘yan kungiyoyin asiri, masu cire sassan mutane domin tsafi da kuma kashe-kashe don tsafi sun zama hanyoyin da ke daukar rayukan mkutane da dama a Nijeriya a wannan lokacin.
A wannan lokacin kuma an lura da cewa, ‘yan Nijeriya da dama suna mutuwa ne a wurane da basu taba yin tunanin zai iya zama musu fagen mutuwa ba, wadannan wurare sune inda ake bayar da tallafi ga al’umma don rage radadin matasalolin tattalin arziki da al’umma suka shiga sakamakon tsare-tsaren tattalin arzikin da kasa ke fuskanta.Wurane ne da mutane ke tururuwa don samun abin da za su sa a bakin salati.
- Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Fitar Da Miliyan 309.5 Don Tallafawa Ɗaliban Da Ke Karatu a Ƙasashen waje
- Yawan Kayayyakin Da Sin Ta Samar Ya Wuce Misali Ko Damuwar Amurka Ta Wuce Kima?
Wata jami’ar Sibil Difen mai suna Fatima Bala, na daga cikin mutum 10 da suka rasa rayukansu a yayin da turmutsitsin da ya auku a wurin raba kayan tallafin abinci a gidan Sanata Aliyu Magatakardan Wamakko a unguwar Gawon Nama cikin birnin Sakwatto a yayin raba tallafin kayan abincin salla.
Rahotannin sun nuna cewa, mutum 30 ne suka ji raunuka daban-daban a turmutsitsin da ya auku a ranar 4 ga watan Afrilu na wannan shekarar.
Yayin da ‘yansanda basu cika daukar matakin hukunci a kan irin wannan lamarin ba, amma jami’yyar PDP a nata bangaren ta nemi a tabbatar da an gudanar da cikakken bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a lamarin, ta kuma yi korafin cewa,wannan ba shi ne karo na farko ba da irin wannan lamarin ke faruwa a gidan tsohon gwamnan wajen raba kayan abinci da nufin tallafa wa al’umma.
“Jami’yyar PDP ta nemi a gudanar da cikakken bincike da nufin samar da tsarin da zai taimaka wajen kiyaye aukuwar irin hakan a nan gaba.
“Wannan ba shi ne karo na farko ba da irin wannan ke faruwa a wurin saboda yadda aka kasa yin cikakken tsarin da zai kare rayuwar al’umma”, wannan wani bangare ne na takardar sanarwar da jami’in wasta labarai na jam’iyyar PDP na Jihar Sakwatto, Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai.
Turmutsitsin da ya auku a gidan Sanata Wamakko na daya daga cikin ireirensa da suka faru a sassan kasar nan, wanda ko a watan da ya gabata wannan jaridar ta yi sharhi a kan haka.
Bangaren sharhin da muka yi a wancan lokacin shi ne kamar haka: “A ranar 24 ga watan Fabrairu lokacin da hukumar kwastam ta fara sayar da shinkafar gwamnati a farashi mai sauki wanda aka yi a ofishita da ke Harbey Road, Yaba, a jihar Legas mutum 7 suka mutu sakamakon turmutsitsin da aka samu a kokkarinsu na sayen shinkafar.An samu matsalar ne yayin da al’umma suka yi shawarar balla kofar ofishin suka yi kokarin shiga don yi wasoso a wannan yanayin ne aka tattake wasu, wasu suka suma.
A wani lamari kuma na irin wannan, mutum 7 ne suka mutu a turmutsitsin da ya auku yayin da gidauniyar ‘AYM Shafa Foundation’ ta yi rabon zakka a garin Bauchi ranar Juma’a 24 ga watan Maris 2024.
Yawancin wadanda suka mutu mata da yara ne wadanda suka yi tururuwa zuwa ofishin gidauniyar da ke hanyar Bauchi zuwa Jos domin karbar zakkar naira dubu goma-goma.
Haka kuma a Jihar Nasara, daliban jami’a 2 suka mutu yayin da gwamnatin jihar ke rabon kayan abinci. Gwamnatin jihar ta sa manyan makarantun jihar ne a cikin wadanda za su amfana da tallafin abinci don rage musu radadin tsadar rayuwar da ake fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur.
Ire-iren wannan turmutsitsin wajen raba tallafin abinci ba sabon abu ba ne, a shekarar da ta gabata mutum 30 suka mutu a yayin da wata kungiya ta kaddamar da rabon abinci a wata coci a garin Fatakwa ta Jihar Ribas.Turmutsitsin ya samo asali ne sakamakon balla shinge da masu shirya rabon abincin suka sa da mutane suka yi ne a yayin rabon abincin.
Haka kuma rahottanin sun nuna cewa, gidauniyar ‘Shafa Foundation’ ta yi irin wannan rabon a watan Ramadan inda wasu mutane suka jikkata.”
A matsayinmu na gidan jarida, muna ganin lamarin a matsayin abin takaici ta yadda irin wannan abin na faruwa amma a ce dukkan jami’an tsaromu su kasa daukar mataki na bincike ko daukar mataki har sai wata jam’iyya da yi korafi.A bayyana lamarin yake kuma cewa, yawancin irin wannan rabon abincin da ake yi a gaban jami’an tsaro ake yin shi.
Muna kara jaddada kiran cewa, duk wata kungiyar da ke shirin bayar da irin wannan tallafin ya kamata ta dauki matakan da suka kamata na kare aukuwar turmutsitsin da zai kai ga rasa rayuwar al’umma.Muna kuma kara jaddada kiran da jam’iyyar PDP ta yi na bukatar ‘yansanda su gudanar da bincike domin gano irin sakacin da aka yi da nufin hukunta duk wadanda yake da hannu wajen mutuwar mutane a wajen rabon tallafin abinci.
A kasa kamar Nijeriya da tsare-tsare gwamnati suka talauta al’ummarta da dama,dole ne a kwana da sanin cewa, duk wata yekuwar bayar da tallafi zata tattaro al’umma masu yawa saboda haka ya kamata a yi isasshen shirin kare rayuwar al’umma.