Rabiu Ali Indabawa" />

Wurin Da Ya Fi Ko’ina Gishiri A Duniya

Tafkin Bahar Mayit ‘Dead Sea’ ya yi matukar shuhra kan tsananin gishiri a ruwansa, amma a duniya shi ne na biyar a jerin wurare masu yawan gishiri.

Idan ka na zaton teku ne ya fi ko’ina gishiri a duniya, kana bisa turba. Kaso biyu cikin uku na duniya ruwane, kuma kaso 96% na ruwan da ke duniya ya na cikin teku. Akwai biliyoyin ton na narkakken gishiri a cikin ruwan teku.
Sai dai yawan gishirin kan bambanta, a kuryoyin Arewa da Kudu, dusar kankara kan narke ta salanta gishirin, a yankunan da ke tsakiyar duniya kuma zafin rana na sa ruwa ya ragu, don haka sai dandanon gishirin ya karu.
Duk da haka akwai wasu wurare a cikin duniyar nan da su ka fi ruwan teku yawan mai dandanon gishiri.
Wanda ya fi shahara a cikinsu shi ne tafkin Bahar Mayit ‘Dead Sea’ da ke kan iyakar Jordan da Isra’ila. dandanon gishirin kogin ya nunka na teku sau 10. Sai dai a jerin wurare masu tsananin gishiri a lamba ta biyar ya tsaya.
Kalmar ‘sea’ a Ingilishi na nufin babban ruwan gishiri da kasa ta yi wa katanga. Shi kuwa ‘Dead Sea’ kasa ta yi masa kawanya ne baki daya, don haka tafki ne amma saboda tsananin gishirinsa ake kiransa ‘teku.’
Duwatsun da ke gabar tafkin na kyalkyali da rana saboda hasken gishirin da ya damfare musu daga ruwan. ‘Baharul Mahid’ shi ne tafki mai tsananin gishiri mafi zurfi a duniya, inda ya ke da zurfin kafa 1,080 daidai da mita 330.
Amma ruwan da ya fi kowanne dandanon gishiri shi ne Kududdufin Don Juan da ke nahiyar Antarctica inda kaso 44% na ruwansa gishiri ne. Ba shi da zurfi ko kadan domin kuwa iyakarsa inchi hudu daidai da santimita 10.
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kai mu

Exit mobile version