Daga Abubakar Abba, Kaduna
Ma’aikatar Wuta da Ayyuka da Gidaje ta bayyana cewar mega wat dubu 2,000 da Gwamnatin Tarayya ta samar amfanin masu amfani da wutar lantarki, don ba a yi tattalin ta ba.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Louis Edozien ya bayyana hakan, inda ya ce, Babban layin wutar lantarki na kasa, ya samar da wutar lamtarki ta kasa, ta samar da mega wat 6,600 daga 750,33 na kasuwancin, sai dai ya ce, ya yi kasa da Mega Wat 4,600 da za a rabawa ma su amfani da wutar.
Edozien ya bayyana hakan ne a garin Jos cikin Jihar Filato lokacin bude taro karo na uku na hukumar samar da wutar lantarki wato (NACOP).
Yace, ana bukatar dimbin kudade domin samar da layikan, ya kuma nuna takaicin sa akan yadda kamfanin samar da wutar wato ‘DISCOs’ akan rashin biyan bashi da ma su amfani da wutar suka ki biyan kamfanin.
Jami’in ya bayyana cewa, taron zai duba karancin raba wutar da layikan ya haifar da kuma duba sauran manyan matsaloli na samar da wutar don a tabbatar da cewa wutar ta kai ga ma su amfani da ita.
Ya yi nuni da cewar dole ne a cike wannan gibin, domin a tabbatar da cewa wutar da aka samar an kara inganta samar da ita.
A karshe ya ce, dimbin bashi da ake bin ma su amfani da wutar da sauran maganar karin kudin wutar za a shawo kan matsalar.
Taron wanda aka fara shi ranar sha takwas ga watan Satumba ana sa ran za a kammala shi a ranar ashirin da biyu na watan Satumba, inda Ministan Maakatar Babatunde Fashola da saura ma su ruwa da tsaki akan harkar wutar lantarki, zasu gabatar da kasidu.