Yau Talata, babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kana shugaban kasar, Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga Thongloun Sisoulith, babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar juyin juya halin jama’ar Laos wato LPRP, kana shugaban kasar, kan cika shekaru 50 da kafa jamhuriyar demokradiyyar jama’ar Laos.
Xi Jinping ya bayyana cewa, jam’iyyar LPRP ta jagoranci jama’ar Laos da hadan kansu wajen yin aiki tukuru, inda ta samu babbar nasara kan harkokin yin gyare-gyare da bude kofa, tare da ci gaba da kyautata rayuwar jama’ar kasar, da kuma samun ingantaccen tasiri a harkokin kasa da kasa.
Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta dade tana daukar Laos a matsayin wata muhimmiyar kasa a fannin diflomasiyyar yankinta, kuma tana son yin aiki tare da Laos, bisa amfani da damar cika shekaru 65 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Laos a shekara mai zuwa, kana za ta ci gaba da bunkasa dangantakar abokantaka ta asali tsakanin kasashen biyu, da karfafa hada kansu, da kuma zurfafawa da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu a sabon zamani, ta yadda za a samar da karin fa’idodi ga mutanen kasashen biyu da kuma bayar da gudummawa ga zaman lafiya da ci gaba a yankin, da ma duniya baki daya. (Safiyah Ma)














