Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga dandalin tattaunawar al’adun Beijing na 2023 a yau Alhamis.
Cikin wasikar tasa, shugaba Xi ya jadadda cewa, al’ummar Sinawa al’umma ce dake da kyawawan al’adun gargajiya masu dogon tarihi. Kuma Sin ta dade da yabawa fahimtar juna, da mutunta juna tsakanin al’adu iri iri.Ya ce Beijing birni ne mai dogon tarihi da al’adu masu dorewa, wanda ke shaida cewa al’adun Sin sun samu ci gaba, da sabuntawa, da hadin kai, da kuma zaman lafiya.
Shugaba Xi ya kara da cewa, Sin za ta kara amfani da fa’idar Beijing a matsayin tsohon babban birni mai tarihi, kuma cibiyar al’adun kasar, wajen inganta mu’amalar al’adu tsakaninta da wurare daban daban na duniya, da inganta ci gaban al’adu, da kiyaye kayayyakin al’adu na tarihi, da kuma mu’amalar al’adu, kana za ta gudanar da ajandar al’adun kasa da kasa, ta yadda za a shigar da karfin al’ada mai zurfi, da dorewa ga inganta gina al’umma mai makomar bai daya ta bil’adama.
Jigon dandalin tattaunawar al’adu na Beijing na 2023 shi ne “Gadon al’adu na-gari, da inganta mu’amala da hadin gwiwa”. Hukumar kula da aikin yada manufofin kwamitin tsakiya na JKS, da kwamitin JKS na reshen birnin Beijing, da kuma gwamnatin al’ummar birnin Beijing suka shirya tare, suka kuma bude shi a yau Alhamis a nan Beijing. (Safiya Ma)