Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da wasu tsoffi na kungiya mai yayata nagartattun ra’ayoyi na “Lao Yang Shu” dake unguwar Yangpu na birnin Shanghai suka aika masa, inda ya bayyana musu kyakkyawan fata.
Xi ya ce, wadannan tsoffi da suka hada da yi ritaya daga hukumomin gwamnati, da makarantu, da rundunonin soja, da masana da dai sauransu, sun ba da darusan tarihi, da yayata ra’ayin kirkire-kirkire na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko JKS, da sauye-sauye masu faranta rai a birnin Shanghai a sabon zamani, bisa ayyukan da suka yi, ko dabarun da suka koya daga zaman rayuwarsu, wanda hakan ke da matukar muhimmanci sosai.
- Habasha Ta Shirya Taron Karawa Juna Sani Karo Na 1 Don Bunkasa Aikin Koyar Da Sinanci
- Trump Da Magoya Bayansa Sun Yi Amfani Da Kalaman Batanci
Xi kuma ya jadadda cewa, jama’a ce ke gina birni, birnin kuma na bautawa jama’a. Yana mai fatan wadannan tsoffi za su ci gaba da bayyana labaransu, ta yadda hakan zai kara azama ga mazauna birnin da su shiga aikin gina birninsu, da kuma shiga aikin daidaita harkokin birni da kafa wani kyakkyawan birni mai jituwa.
A watan Nuwamban shekarar 2019, yayin da shugaba Xi Jinping ya ziyarci birnin Shanghai, a karon farko ya gabatar da ra’ayin “Jama’a ce ke gina birni, birnin kuma na bautawa jama’a”, daga baya ya ba da umurni game da aikin raya birnin.
Mambobin kungiyar yayata nagartattun ra’ayoyi na “Lao Yang Shu” wadanda suka yi ritaya daga bangarori daban-daban, sun rubuta wata wasika kwanan baya ga shugaban kasar Sin, inda suka bayyana masa yadda suke gudanar da ayyukansu, da ma niyyarsu ta ingiza aikin raya birnin a matsayin ’yan JKS. (Amina Xu)