Shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi a taron bikin murnar cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong karkashin Jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin kaddamar da sabuwar gwamnatin yankin ta 6.
Xi Jinping, wanda shi ne shugaban kwamitin koli na JKS, kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya taya John Lee, sabon jami’in farko na gwamnatin yankin da manyan jami’ai da mambobin majalisar zartarwar sabuwar gwamnatin yankin murna.
Shugaban ya ce aiwatar da manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu” ta haifar da nasarorin da kowa ke iya gani a yankin HK. Kuma tun bayan dawowarsa karkashin kasar Sin, yankin ya bayar da gagarumar gudunmawa ga bunkasar tattalin arzikin kasar mai dogon zango cikin sauri da kuzari ba tare da tangarda ba.
Haka kuma, HK ya zama wani muhimmin bangare ga ci gaban kasar Sin, wanda ya yi daidai da dabarun raya kasar. Baya ga haka, ya ci gaba da rike matsayinsa na mai karfi da bayar da ’yanci da bude kofarsa, tare kuma da kiyaye dokokin kasa da kasa.
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce, yankin HK ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa sabon fagen fadada da zurfafa manufar bude kofa ta kasar Sin a karin bangarori.
Kana, HK ya zama jigon saurin ci gaban bangaren kimiyya da fasaha da kirkire kirkire, haka kuma ya samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya kai mizanin kasa da kasa.
Har ila yau, ya ce, an kare tare da kyautata dokokin da ake amfani da su a yankin, kuma al’ummarsa sun kasance tsintsiya madaurinki daya.
A cewarsa, tsarin demokradiyyar HK da ya dace da manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu”, da kundin tsarin mulkin yankin, shi ne mafi dacewa wajen kare hakkokin demokradiyya na mazauna yankin da kuma tabbatar da ci gaba da kwanciyar hankalinsa.
Ya ce manufar “Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu”, abu ne da aka ga alfanunsa cikin lokaci mai tsawo, don haka babu dalilin sauya ingantaccen tsari irinsa, haka kuma, dole ne a ci gaba da rungumarsa.
Ban da wannan kuma, jami’an sabon gwamnatin yankin sun yi rantsuwar kama aikinsu a bikin. (Fa’iza Mustapha)