Da safiyar yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da manyan jami’an muhimman kungiyoyin tattalin arziki na kasa da kasa dake halartar taron tattaunawa na “1+10”, wanda aka bude a nan birnin Beijing.
Xi Jinping ya ce, ya kamata kasashe daban-daban su dauki ci gaban sauran kasashe a matsayin damammaki a maimakon kalubale, ta yadda za a mai da hankali kan dunkulewar duniya, da hadin gwiwa, da cin moriya tare a wannan zamani.
- Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Bayar Da Belin Yahaya Bello
- An Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Kan Hakkin Tattalin Arziki Da Al’Umma Da Al’Adu Na Kasa Da Kasa a Birnin Hangzhou
Ya ce Sin na fatan kara hadin gwiwa da wasu muhimman kungiyoyin tattalin arziki na kasa da kasa, don aiwatar da manufar gudanar da harkoki tsakanin mabambantan bangarori, da ingiza hadin gwiwar kasa da kasa, da goyon bayan bunkasuwar kasashe masu tasowa, da saurin bunkasuwa, da gaggauta raya duniya dake da madogara da yawa, mai daidaito bisa zaman oda da doka, da dunkulewar tattalin arzikin duniya mai kawo amfani ga mabambantan bangarori, da raya wata duniya mai adalci dake bunkasa tare.
Shugaban sabon bankin samar da ci gaba wato NDB, da shugabar IMF, da shugaban bankin duniya, da babbar jami’ar kungiyar WTO, a madadin bangarori masu tsaki da ruwa sun gabatar da jawabai yayin zaman. Inda suka jinjinawa ci gaban tattalin arzikin Sin, da bayyana kyakkyawan fata ga makomar bunkasuwar Sin, kana da bayyana godiya ga goyon bayan da Sin ta dade tana baiwa kungiyoyin tattalin arzikin kasa da kasa.
Muhimman kungiyoyin tattalin arziki na kasa da kasa na fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin, da nacewa ga manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin mabambantan bangarori, da raya makomar Bil Adama ta bai daya tare.
Xi Jinping ya saurari jawaban da wakilan kungiyoyin suka gabatar daga zuciya, kuma ya ba da amsa ga wasu batutuwan da suke jawo hankalin kasa da kasa. Alal misali tattalin arzikin duniya da na kasar Sin, da yadda za a daidaita harkokin duniya da sauransu. (Amina Xu)