Da yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwararsa ta kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wadda ta zo kasar Sin don ziyarar aiki. Shugabannin biyu sun sanar da daga matsayin huldar dake tsakanin kasashensu wato Sin da Tanzaniya zuwa wani babban kawancen hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp