Yau Laraba, 8 ga wata bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da uwar gidansa Peng Liyuan sun halarci liyafar maraba da shugaban Serbia Aleksandar Vučić da uwar gidansa suka shirya a Belgrade.
Xi Jinping ya yi wani jawabi a yayin liyafar, inda ya bayyana cewa, a yanzu haka, a karkashin jagorancin shugaba Vučić, gwamnatin Serbia da al’ummar kasar sun yi aiki tukuru tare da samun nasarori masu ban mamaki a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa da inganta rayuwar jama’a. Ya ce a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, Sin da Serbia sun kara karfi kan raya shawarar Ziri daya da hanya daya, tare da cimma nasarori masu yawa a fannin, wanda ya zama kyakkyawan misali na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama.
Baya ga haka, Xi Jinping ya kara da cewa, kafin liyafar, ya yi cikakkiyar ganawa mai zurfi tare da shugaba Vučić kuma sun cimma matsaya mai muhimmanci. Kazalika sun rattaba hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa tare da sanar da kafa al’ummar Sin da Sabiya mai kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani, da daga dangantakar dake tsakanin Sin da Serbia zuwa wani sabon matsayi. (Bilkisu Xin)