Za a wallafa wata mukala da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta, wanda ke karfafa gwiwar matasan sabon zamani su dauki nauyin daukaka zamanantar da kasar Sin cikin jarumta.
Za a wallafa mukalar ce gobe Alhamis, cikin bugu na 9 a bana na mujallar Quishi, wadda ta kasance mallakar JKS.
- Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
- NEMA Ta Karɓi ‘Yan Nijeriya 203 Da Suka Maƙale A Libya
Mukalar na bayyana rawar kungiyar matasa ta JKS wajen jan hankalin jama’a, domin su bayar da gudummuwa ga gina kasa mai karfi da cimma burin kasar na farfadowa.
A cewar mukalar, ya kamata matasa su kasance kan gaba, kuma muhimmin karfi a bangarorin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da farfado da kauyuka da kare muhalli da hidimtawa al’umma da kare kasa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp