A yau Laraba ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sako zuwa ga takwaransa na tarayyar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, don nuna alhinin rasuwar tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari, inda a madadin gwamnati gami da jama’ar kasar Sin, shugaba Xi ya mika ta’aziyya zuwa ga iyalan marigayin, da gwamnatin Najeriya da kuma jama’ar kasar baki daya.
A sakon nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, marigayi Buhari, muhimmin jagora ne na Najeriya, kana mutum ne mai kwarjini a duniya, wanda ya dukufa kan lalubo wa Najeriya hanyar ci gaba, tare da bayar da babbar gudummawa ga hadin-kan al’ummomin kasar da samun ci gabanta.
Ya ce, Buharin ya tsaya tsayin daka ga karfafa zumunta tare da kasar Sin, da taimaka wa sada zumunci tsakanin Sin da Najeriya, har ma da inganta hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Rasuwar Muhammadu Buhari, babban rashi ne ga jama’ar Najeriya, kuma jama’ar kasar Sin sun rasa wani babban aboki.
Xi ya kara da cewa, kasar Sin na maida hankali sosai ga ci gaban dangantakarta da Najeriya, kuma tana mai fatan yin kokari tare da Najeriya, don sa kaimi ga bunkasar dangantakar kasashen biyu daga dukkan fannoni kuma bisa manyan tsare-tsare. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp