Jiya Jumma’a da dare, bisa agogon Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi hira da zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump, ta wayar tarho, bisa gayyatar da aka yi masa.
A yayin hirarsu, shugaba Xi ya taya Mista Trump murnar sake lashe zaben shugabancin kasar Amurka, kana ya yi fatan ganin huldar dake tsakanin kasashensu 2 ta samu ci gaba a sabon wa’adin aiki na Mista Trump a matsayin shugaban kasar Amurka.
- SIMDA Ta Ƙulla Alaƙa Da Jami’ar Skyline Kan Ci Gaban Ilimi Da Kasuwancin Zamani A Kano
- Fahimtar Manufofin Nijeriya A Kasashen Waje A Karkashin Tuggar
A cewar shugaban na Sin, dukkan kasashen 2 na da burin kyautata zaman rayuwar al’umma. Sa’an nan ta la’akari da babbar moriyarsu ta bai daya da damammaki na hadin kai da suka samu, tabbas kasashen 2 za su iya zama aminai dake amfanar da juna, tare da samar da alfanu ga al’ummun duniya.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kasashen Sin da Amurka suna cikin mabambantan yanayi ne, don haka ba za a rasa bambancin ra’ayi tsakaninsu ba, amma abun da ya fi muhimmanci shi ne su lura da babbar moriyar juna, da lalubo bakin zaren warware matsalar da ake fuskanta. Kana ya ce, ya kamata kasashen 2 su gimama juna, da kokarin hadin gwiwa, gami da daukar matakan da za su amfanar da dukkansu, da sauran kasashe daban daban.
A nasa bangare, Donald Trump ya ce yana darajanta abokantakar dake tsakaninsa da shugaba Xi na kasar Sin. Kuma kamata ya yi kasashen 2 su kiyaye hulda mai kyau, da hadin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya a tsakaninsu.
Ban da haka, shugabannin 2 sun yi musayar ra’ayi kan wasu batutuwan da suke jan hankulansu, kamar su yakin da ake yi a kasar Ukraine, da rikicin Isra’ila da Falasdinu, da dai sauransu. (Bello Wang)