Da yammacin yau Alhamis ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, ya ziyarci mambobin taro na uku na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wato CPPCC karo na 14 ta kasar Sin, wadanda suka zo daga kungiyar dimokuradiyya ta kasar Sin, da kungiyar raya dimokuradiyya ta kasar Sin, da kuma bangarorin ilimi. Shugaban na Sin ya kuma halarci taron kungiyar hadin gwiwa na CPPCC, domin sauraron ra’ayoyi da shawarwari.
Yayin ziyartar mambobin majalisar ta ba da shawara kan harkokin siyasa, Xi ya jadadda cewa, ya kamata a karfafa amfani da ilmi don inganta kimiyya da fasaha da kuma kwararru, ta yadda za a kafa wani yanayi na amfani da kwararru baki daya.
Bugu da kari, albarkacin bikin ranar mata ta kasa da kasa mai zuwa, a madadin kwamitin kolin JKS, Xi Jinping ya mika sakon gaisuwa da fatan alheri ga wakilai mata, da mambobi mata, da ma’aikata mata da suka halarci manyan taruka biyu, da mata na dukkan kabilu, da na dukkan sassan kasar, da ‘yan uwa mata na yankin musamman na Hong Kong, da na yankin musamman na Macao, da na yankin Taiwan, da kuma Sinawa mata dake rayuwa a kasashen waje. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp