Taron kolin Kungiyar Hadin Kai ta Shanghai SCO na shekara ta 2025 zai gudana daga ranar 31 ga watan Agusta zuwa 1 ga watan Satumba a birnin Tianjin na kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai jagoranci taron majalisar shugabannin kasashe membobin SCO karo na 25 da kuma taron “SCO+” inda zai gabatar da jawabi mai muhimmanci.
Da safiyar yau Juma’a mai ba da taimako ga ministan harkokin wajen Sin Liu Bin ya bayyana cewa, a karo na biyar, Sin za ta shirya taron kolin SCO, kuma zai zama mafi girma a tarihin kungiyar tun bayan kafuwarta.
Liu Bin ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da ma’aikatar harkokin wajen Sin din ta gudanar.
A lokacin taron, Shugaba Xi zai kuma shirya liyafar maraba ga shugabannin da suka halarci taron da kuma wasu ayyukan da suka shafi dangantakar Sin da kasa da kasa. Kuma a yayin taron na SCO, Shugaba Xi Jinping zai hadu da shugabannin kasashe fiye da 20 da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa 10 a birnin Tianjin.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp