ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Ya Amsa Wasikar Ma’aikatan Kamfanin Samar Da Karafa Na Smederevo Dake Serbia

by CGTN Hausa
2 years ago
Xi

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da wasu ma’aikata ‘yan kasar Serbia, na masana’antar samar da karafa ta Smederevo na kasar, wanda ke karkashin mallakar kamfanin HBIS na kasar Sin, suka aika masa, inda ya karfafa musu gwiwa, don su ci gaba da samar da gudunmowa a kokarin karfafa zumunta tsakanin kasashen Sin da Serbia.

A cewar shugaban na kasar Sin, yayin da ya kai ziyara kasar Serbia a shekarar 2016, ya ziyarci masana’antar samar da karafa ta Smederevo, inda ya yi hira da wasu ma’aikata, wadanda a lokacin suka nuna goyon bayansu ga hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Serbia, da bayyana kyakkyawan fata game da makomar masana’antarsu.

  • Ba Za A Raba Ci Gaban Kasar Sin Da Gudunmuwar Mata Ba

Shugaba Xi ya ce, bisa wasikar da wasu ma’aikatan masana’antar suka aika masa, ya san cewa, harkokin masana’antar sun samu ci gaba sosai, bisa kokarin aiki da jami’ai da ma’aikata na kasashen Sin da Serbia suke yi, wanda ya taimakawa kokarin raya tattalin arziki a birni na Smederevo. Har ila yau, shugaban ya ce yana farin ciki matuka, ganin yadda masana’antar samar da karafar ta fara samun riba cikin sauri, da kare guraben aikin yi na ma’aikata fiye da 5000, gami da tabbatar da jin dadin zaman rayuwar wasu magidanta fiye da 1000, bayan wani kamfanin Sin ya zuba jari a masana’antar.
Kafin haka, wasu ma’aikata ‘yan kasar Serbia 30, na masana’antar samar da karafa ta Smederevo, sun rubuta wata wasika ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, a madadin sauran ma’aikatan masana’antar, inda suka yi bayani kan yanayin da harkokin masana’antar ke ciki, da gudunmowar da ta samar a fannin kyautata rayuwar jama’ar wurin. Ban da haka, sun mika godiya ga shugaban na Sin, kan yadda ya kula da aikin zuba jari ga masana’antar samar da karafa ta Smederevo, gami da tabbatar da kammaluwar aikin. (Bello Wang)

ADVERTISEMENT
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya
Daga Birnin Sin

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Daga Birnin Sin

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Next Post
An Kira Taron Dandalin Tattaunawa Kan Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Faransa

An Kira Taron Dandalin Tattaunawa Kan Musayar Al'adu Tsakanin Sin Da Faransa

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025
Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

November 14, 2025
Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

November 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.