Xi Jinping, sakatare janar na kwamitin kolin JKS, ya nanata bukatar yayata muhimmin ruhin kafuwar JKS da ruhin Yan’an, tare da kokari cikin hadin kai, domin cimma burika da ayyukan da babban taron wakilan JKS karo na 20 ya gabatar.
Ya ce ruhin Yan’an na bayyana imani mai karfi kan daidaitacciyar alkiblar siyasa, da kyautata tunani da neman gaskiya bisa shaidu, da burin hidimtawa jama’a bil hakki da gaskiya da ruhin dogaro da kai da kuma aiki tukuru.
A cewarsa, ruhin, da kuma al’adu masu daraja da da’ar da aka samar tare da yayatawa a zamanin da JKS ta mayar da Yan’an a matsayin hedkwatarta, dukiyoyi ne masu kima ga jam’iyyar, kuma ya kamata a gaje su daga zuri’a zuwa zuri’a. (Fa’iza)